Trends

IMF Zai Rage Hasashen Tattalin Arziki na Duniya

Asusun Lamuni na Duniya, International Monetary Fund (IMF), ya bayyana cewa zai rage hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya sakamakon ci gaba da rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran, wanda ke kawo tangarda ga harkokin tattalin arziki da kuma jinkirta dawowar farashi yadda suke kafin rikicin.

Daraktar gudanarwa ta IMF, Kristalina Georgieva, ta ce rikicin na haifar da “matsaloli marasa daidaito” ga kasashe daban-daban, tana mai gargadin cewa farashi ba zai dawo da sauri yadda yake kafin rikicin ba.

Ta ce girman rage hasashen zai danganta ne da tsawon lokacin rikicin da kuma yadda ake iya dawo da samar da kayayyaki kamar yadda yake a baya. Ta kuma kara da cewa ko da an samu tsagaita wuta, dawowar tattalin arziki ba zai zama iri daya a ko’ina ba, lamarin da zai tsawaita matsin farashi tare da wahalar da bankunan tsakiya wajen tsara manufofi.

Fargaba ta karu bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da kulle mashigin ruwa na Strait of Hormuz gaba daya ta hanyar sojojin ruwa, wanda ke da muhimmanci wajen jigilar man fetur. Wannan mataki ya kara haddasa fargabar tangardar samar da mai da kuma rikicewar kasuwannin duniya.

Trump ya ce an dauki matakin ne bayan tattaunawa da Iran a Pakistan ta kasa cimma matsaya, yana mai zargin Tehran da kin janye shirin nukiliyarta.
Matakin ya jefa shakku kan dorewar tsagaita wutar da aka cimma a makon da ya gabata, tare da rage fatan samun mafita mai dorewa, yayin da masana ke gargadin yiwuwar karin tashin farashin makamashi.

A baya, World Bank ya rage hasashen ci gaban tattalin arzikin yankin Afrika kudu da Sahara na 2026 da kaso 0.3 zuwa kashi 4.1, yana mai danganta hakan da karuwar farashin mai da taki da kuma dimbin bashin da ke da nasaba da rikicin Iran.

Masu tsara manufofi a duniya na fargabar cewa rikicin zai iya rusa kokarin farfadowar tattalin arziki, musamman a kasashe masu tasowa da ke fama da tsadar rayuwa da matsalolin samar da kayayyaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *