Category: Politics
Har Yanzu Ina PDP, Zan Mara Wa Kowane Tafiyan Da Zai Kori APC a 2027 – Sule Lamido
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), amma yana da niyyar mara baya ga kowanne irin tsari da zai taimaka wajen kifar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga mulki a shekarar 2027. Yayin wata hira da aka yi da shi a shirin…
Safarar Miyagun Kwayoyu: Kwamishinan Harkokin Sufuri na Jihar Kano Ya Yi Murabus
Kwamishinan Harkokin Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye mukaminsa sa’o’i bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ke nazarin rawar da ya taka a batun bayar da beli ga wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. Wannan mataki na murabus ana kallonsa a…
Zaben 2027: INEC Ta Gargadi APC, PDP, ADC da Sauran Jam’iyyu Kan Kamfen Ba Bisa Ka’ida Ba
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gargadi jam’iyyun siyasa da su guji fara yakin neman zabe da wuri domin zaben 2027, tana mai bayyana hakan a matsayin karya dokar zabe. Mai magana da yawun shugaban INEC, Mista Rotimi Oyekanmi, ne ya fitar da wannan gargadi a wata hira da aka yi da…
Zaben 2027: Shawarar Umahi Ga Kabilar Igbo Mu Jira 2031, Yanzu ba Lokacin mu Ba
Ministan Ayyuka na Tarayya, Sanata Dave Umahi, ya bayyana cewa duk da cewa yankin Kudu maso Gabas zai samu damar fitar da shugaban kasa a nan gaba, wannan dama ba za ta zo ba a zaben shekarar 2027. A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Umahi ya bukaci al’ummar Kudu maso Gabas da…
Zaben 2027: Tabbas Muna Tunanin Tsayar da Jonathan / Kwankwaso – Shugaban PDP
Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa domin tsayar da tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben shekarar 2027. Tun bayan rashin nasararsa a zaben 2015, Jonathan ya dan nesanta kansa daga harkokin siyasa. Sai dai rahotanni…
Yan adawa Na Amfani da Matsalar Tsaro Don Cin Moriyar Siyasa – Mataimakin Gwamnan Sokoto
Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto, Injiniya Idris Mohammed Gobir, ya zargi jam’iyyun adawa da yin amfani da matsalolin tsaro da ke addabar wasu sassan jihar don cimma manufofin siyasa kafin zaben shekarar 2027. Gobir ya bayyana hakan ne yayin wani taron horo na yini guda da aka shirya wa masu amfani da kafafen sada zumunta na…
Rikicin PDP Ya zo Karshe a Halin Yanzu – Wike
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, a ranar Litinin ya bayyana cewa rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ya lafa a halin yanzu, sakamakon ficewar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar. Wike ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja, inda ya mayar da martani kan…
Tsoffin Sojojin Isra’ila Sun Nemi Trump Ya Matsawa Netanyahu Don Kawo ƙarshen Yaƙin Gaza.
Tsaffin jami’an tsaron na Isra’ila sun bayyana buƙatar tasu ce cikin buɗaɗɗiyar wasiƙar da suka aika wa shugaban na Amurka, inda suka bayyana cewa dogon nazarin da suka yi a matsayinsu na ƙwararru kan sha’anin tsaro, ya basu damar samun tabbacin cewar, a halin yanzu ƙungiyar Hamas ba ta tattare da wata barazana ga Isra’ila….
LG Polls: Rudani Yayin da Mambobin PDP Suke Fitowa a Matsayin ‘Yan Takarar APC a Rivers
Ana cikin wani hali na rudani a Jihar Rivers gabanin zaben kananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga Agusta, 2025, bayan da aka gano cewa wasu mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun bayyana a matsayin ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomi na All Progressives Congress (APC) a yawancin kananan hukumomin jihar. Bincike…
Zaben 2027: Tinubu Wa’adi Biyu Zai Yi ‘Yan Arewa Ku Jira Zuwa 2031 – Sen Akume
Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya bukaci ‘yan siyasar Arewacin Najeriya da su dakata da burin neman kujerar shugaban kasa har zuwa shekara ta 2031. Akume ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa na tsawon kwanaki biyu kan hulɗar gwamnati da ‘yan kasa, wanda aka gudanar a Kaduna ranar Talata, karkashin shirya…

