Tsoffin Sojojin Isra’ila Sun Nemi Trump Ya Matsawa Netanyahu Don Kawo ƙarshen Yaƙin Gaza.

Tsaffin jami’an tsaron na Isra’ila sun bayyana buƙatar tasu ce cikin buɗaɗɗiyar wasiƙar da suka aika wa shugaban na Amurka, inda suka bayyana cewa dogon nazarin da suka yi a matsayinsu na ƙwararru kan sha’anin tsaro, ya basu damar samun tabbacin cewar, a halin yanzu ƙungiyar Hamas ba ta tattare da wata barazana ga Isra’ila.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito tsaffin jami’an tsaron na cewa, da fari yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar kan Hamas a Gaza yana kan daidai domin kare kanta daga duk wata baraza, to amma bayan muradun ta data cimma, ci gaba da yaƙin ya tashi daga na neman kare kai, ma’ana dai yaƙin ya rikiɗe kenan zuwa zalunci.

Cikin wani bidiyon haɗin gwiwa da suka fitar, tsaffin shugabannin hukumomin tsaron Isra’ila sun yi gargaɗin cewa ana ci gaba da jan ƙafa wajen kawo ƙarshen yaƙin Gaza ne saboda dalillai na siyasa, kuma a halin da ake ciki, Isra’ila na tafka hasara fiye da nasarorin da take samu a yaƙin.

Tsohon shugaban Hukumar Leƙen Asrin Isra’ila Amos Malka, ya ce kamata ya yi a ce a yanzu ƙasar ta fi shekara guda da kawo ƙarshen yaƙin Gaza, duba da nasarorin da ta samu cikin ƴan watanni bayan ƙaddamar da yaƙin.