Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya bukaci ‘yan siyasar Arewacin Najeriya da su dakata da burin neman kujerar shugaban kasa har zuwa shekara ta 2031.
Akume ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa na tsawon kwanaki biyu kan hulɗar gwamnati da ‘yan kasa, wanda aka gudanar a Kaduna ranar Talata, karkashin shirya Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation.
A cewarsa, babu buƙatar ‘yan siyasar Arewa su yi tunanin takarar 2027, domin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi nasarori masu yawa kuma yana kan tafarkin kawo ci gaba a ƙasar.
“Tinubu ya na tafiya da kowa, kuma ya bai wa yankin Arewa damammaki da dama a cikin gwamnatin sa. Maganar cewa Arewa ba ta da wakilci gaskiya ba ce,” in ji Akume.
Ya kara da cewa: “Hanyar mota daga Sokoto zuwa Bagary ta fi ta Legas zuwa Calabar tsawo – wannan na nuna irin kulawar da ake bai wa Arewa.”
Akume ya ce gwamnatin Tinubu ta shafe shekara biyu da watanni biyu a kan karagar mulki, kuma nasarorin da aka samu na da muhimmanci matuka.
“Tinubu ya yi alkawarin nuna adalci a mulki, kuma har yanzu bai karya wannan alkawari ba. Ya kamata a ci gaba da goyon bayan wanda yake yin abin da ya dace, domin ya ƙara yin ƙoƙari.”
Ya koka kan yadda wasu kafafen watsa labarai ke yada bayanan da ba su dace ba dangane da gwamnatin Tinubu, yana mai cewa gwamnatin ta samu nasarori wajen rage farashin abinci, bunkasa tsaro da inganta ababen more rayuwa.
Akume ya ce: “Tinubu yana kan tafarkin kai Najeriya zuwa ƙasar da aka yi mafarki. Saboda haka, ina roƙon ‘yan siyasar Arewa da su jira har sai 2031 kafin su fito takara.
“Kada ku shiga sahun waɗanda za su dakile ci gaban da ake samu a halin yanzu.”
Ya kuma jaddada cewa cire tallafin mai ya bai wa gwamnati dama da ƙarin kuɗi a matakin jihohi domin aiwatar da manyan ayyuka da samar da dimokuraɗiyya ta gaskiya.
Sanata Akume ya bayyana cewa ajandar Renewed Hope ba wata kalma ba ce kawai, illa dai wata manufa ce da ke ƙoƙarin dawo da bege da ci gaba ga kowane yanki na ƙasa.
Ya ambaci wasu daga cikin nasarorin da aka samu a fannoni daban-daban kamar diflomasiyya da manufofin kasashen waje, sufuri, samar da ayyukan yi, ilimi, gyaran haraji, ‘yancin kananan hukumomi, tsaro, wasanni, yaƙi da cin hanci, zaman lafiya da sauran su.
A karshe, ya jaddada cewa: “Tinubu ya kafa tubalin sabuwar Najeriya ta hanyar hangen nesa da jajircewa don samar da dimokuraɗiyyar da ta shafi kowa. Ya kamata ‘yan siyasa masu kishin ƙasa su jinkirta burin su na kujerar shugabanci har zuwa 2031.”



