SDP Ta Karyata Jita-Jitar Dakatar da El-Rufai, Ta Gargadi Jama’a Kan Labarun Karya

Mallam Nasir El-Rufai

Reshen Jihar Kaduna na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ya musanta rade-radin da ke yawo cewa an dakatar ko kuma an kore tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai daga jam’iyyar. Jam’iyyar ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya mai tushe daga siyasa da nufin yaudarar jama’a da kuma tayar da zaune tsaye a cikin jam’iyyar.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin ta hannun Hon. Darius Kurah, Sakatare na Ƙasa mai magana da yawun jam’iyyar a jihar Kaduna, SDP ta bayyana rahoton a matsayin ƙirƙirarren labari da aka gina don rikita al’umma da haifar da rudani a jam’iyyar.

Kurah ya bayyana cewa wani da ake kira Araba Rufus Aiyenigba, wanda aka danganta masa wannan sanarwa da cewa shi ne mai magana da yawun SDP na ƙasa, ba shi da wannan matsayi.

“Araba Rufus Aiyenigba ba shi ne National Publicity Secretary na jam’iyyar SDP ba,” in ji Kurah. “Ambasada Judith Shua’ibu ce ke rike da wannan matsayi, kuma duk wata sanarwa da Aiyenigba ya fitar da’awar cewa daga jam’iyyar SDP ce, ba ta da inganci, ba ta da sahihanci kuma ba ta da tasiri.”

Kurah ya ƙara da cewa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanadi hanyoyi bayyanannu na ladabtar da membobi, kuma babu ɗayansu da aka bi a batun da ya shafi El-Rufai.

A cewarsa, babu wata wasika ko kira da aka aika wa El-Rufai daga kwamitin ladabtarwa, kuma ba a kore shi daga kowanne matakin jam’iyyar ba — daga matakin gunduma har zuwa Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC).

SDP ta kuma yi watsi da jita-jitar cewa El-Rufai na yi wa jam’iyyar zagon ƙasa ta hanyar tallafa wa wasu jam’iyyun adawa. “Wannan tuhuma maras tushe ce kuma ba ta da wata hujja,” in ji sanarwar. Kurah ya bayyana cewa duk da cewa El-Rufai ya cika dukkan sharuɗɗan zama memba a jam’iyyar, bai riƙe ko nemi wani muƙami a jam’iyyar ba.

Kurah ya zargi wasu mutane da haɗin gwiwa da wasu magoya bayan jam’iyyar APC da nufin haddasa rikici a cikin jam’iyyar.

“Wannan ƙarya da aka baza a kafafen watsa labarai alama ce ta yunkurin siyasa da ke neman janyo rudani a tsakanin mambobin jam’iyyar da kuma al’umma gaba ɗaya,” in ji Kurah.

Jam’iyyar SDP reshen Jihar Kaduna ta roƙi mambobinta da al’umma su yi watsi da wannan labari mara tushe, wanda ta ce yunkuri ne na kawo rikici da jawo hayaniya a siyasar ƙasa gabanin zaɓen 2027.

“Babu wani matakin ladabtarwa da aka ɗauka akan Malam Nasir El-Rufai, kuma muna roƙon ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da su yi watsi da irin wannan labarin ƙarya,” in ji Kurah a ƙarshe.