Trends

Gwamna Yusuf ya amince da nadin sabbin shugabannin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars

Nigeria's captain Ahmed Musa speaks during the pre-match press conference in Garoua on January 10 2022. (Photo by Daniel Beloumou Olomo / AFP) (Photo by DANIEL BELOUMOU OLOMO/AFP via Getty Images)

Wannan nadin ya biyo bayan karewar wa’adin kwamitin baya da kuma rushewar sa da aka yi kwanan nan.

Sanarwar nadin ta fito ne daga mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a ranar Lahadi.

A cewar sanarwar, sabbin mambobin kwamitin an zabe su ne bisa cancanta da kwarewar su a fagen gudanarwa, kuma za su yi aiki na tsawon shekara guda a matsayin rikon kwarya, tare da yiwuwar sabunta wa’adinsu idan aka ga sun taka rawar gani a kakar wasanni mai zuwa.

Sabbin mambobin kwamitin sun hada da:

Ali Muhammad Umar (Nayara Mai Samba) – Shugaba

Salisu Kosawa – Mamba Mai Girma (Honorary Member)

Yusuf Danladi (Andy Cole) – Mamba

Nasiru Bello – Mamba

Muhammad Ibrahim (Hassan West) – Mamba

Muhammad Usman – Mamba

Muhammad Danjuma Gwarzo – Mamba

Mustapha Usman Darma – Mamba

Umar Dankura – Mamba

Sauran sun hada da:

Ahmad Musbahu – Mamba

Rabiu Abdullahi – Mamba

Abubakar Isah Dandago Yamalash – Daraktan Harkokin Yada Labarai

Ismail Abba Tangalash – Mataimakin Daraktan Yada Labarai

Injiniya Usman Kofar Naisa – Mamba

An bayyana cewa an zabi wadannan mutane ne don bunkasa ci gaban kungiyar da tabbatar da ingantaccen tafiyar da al’amuran kungiyar a sabon zamani.