Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (Nigeria Football Federation) ta bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince Najeriya ta karbi bakuncin taron Majalisar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) da kuma bikin bayar da kyaututtuka na shekarar 2026, wanda aka shirya gudanarwa a watan Oktoba.
Wadannan bukukuwa za su biyo bayan taron babban majalisar CAF na 48, wato CAF Ordinary General Assembly.
A cewar NFF, Shugaba Tinubu ya bayyana aniyarsa ta karɓar bakuncin taron ne a taron Africa Forward Summit da aka gudanar a Nairobi, Kenya, bayan ganawarsa da shugaban CAF, Patrice Motsepe.
A taron, an samu halartar Ministan Harkokin Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu, shugaban NFF, Ibrahim Musa Gusau, mai ba shugaban CAF shawara, Amaju Pinnick, da kuma Mukaddashin Sakatare Janar na CAF, Samson Adamu.
Taron CAF Ordinary General Assembly na tattaro manyan shugabannin kwallon kafa daga kasashe mambobi 54 na CAF, tare da wakilan yankuna shida na ƙungiyar da kuma manyan jami’an kwallon kafa daga sassan nahiyar Afirka.
