Shugaban jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana dalilan da suka hana tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, da jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, shiga PRP gabanin zabukan shekarar 2027.
Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata shirya siyasa ta Hausa a tashar DITV Kaduna, inda ya ce tattaunawar da aka yi tsakanin PRP da ‘yan siyasar biyu ta rushe ne sakamakon sabani kan sharuddan shiga jam’iyyar.
Ya ce Obi da Kwankwaso sun nemi hadin gwiwa da PRP, kuma an kai matakin kafa kwamitin da zai ci gaba da tattaunawa, amma daga baya aka samu matsala.
A cewarsa, daya daga cikin manyan batutuwan da suka haddasa rashin jituwa shi ne bukatar su na a ba su tikitin takarar shugaban kasa kai tsaye ba tare da shiga gasar cikin jam’iyya ba.
“Sun ce kafin su shiga jam’iyyar, su ne ‘yan takarar shugaban kasa, wato a ba su tikiti kai tsaye,” in ji shi. “Mun ce musu wannan ba tsarin PRP ba ne.”
Shugaban PRP ya kara da cewa jam’iyyar ta dage cewa dole ne su fara shiga jam’iyyar a hukumance sannan su bi tsarin cikin gida kafin neman mukami ko tikiti.
Ya ce: “Ka fara shigowa jam’iyya, sannan daga baya ka ce ka na so ka tsaya takara. Amma ba za ka zo tun farko ka nemi a baka tikiti ba tare da gasa ba.”
Baba-Ahmed ya kuma ce bangarorin biyu sun nemi a ba su manyan mukamai a jam’iyyar saboda magoya bayansu da suke shirin kawowa PRP.
Sai dai ya ce jam’iyyar ta ki amincewa da hakan, tana mai jaddada cewa dole ne a bi ka’idojin jam’iyyar da tsarin dimokuradiyya na cikin gida.
Ya kuma bayyana cewa an samu wasu matsaloli da suka hada da batun matsayin PRP a shafin hukumar INEC da kuma rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar, wadanda suma suka taka rawa wajen rushe tattaunawar.
Duk da haka, ya ce bangarorin biyu sun rabu cikin lumana ba tare da sabani ko rikici ba.
