Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Sama ta Najeriya (NUPRC) ta bayyana cewa yawan danyen man da Najeriya ta hako a watan Afrilun 2026 ya karu zuwa matsakaicin ganga miliyan 1.663 a rana, ciki har da condensates.
Wannan ya nuna karin ci gaba idan aka kwatanta da watan Maris, lokacin da kasar ta samar da ganga miliyan 1.546 a rana, lamarin da ke nuna ingantuwar ayyukan hakar mai da karin yawan samarwa daga manyan rijiyoyin mai.
Rahoton ya nuna cewa danyen mai kadai ya kai ganga miliyan 1.488 a rana, wanda ya kusa kai Najeriya ga cika kaso miliyan 1.5 da kungiyar OPEC ta ware mata.
Condensates kuwa sun bayar da gudunmawar ganga 174,873 a rana, wanda ya kara yawan jimillar samar da man ruwa da kashi 7.58 cikin 100 idan aka kwatanta da watan da ya gabata.
NUPRC ta bayyana cewa manyan rijiyoyin da suka fi bayar da gudunmawa wajen fitar da mai sun hada da Bonga mai ganga miliyan 3.06, Erha ganga miliyan 2.05, Anyala-Madu ganga miliyan 1.81, Utapate ganga miliyan 1.78, Egina ganga miliyan 1.47, da kuma sabon nau’in Cawthorne crude mai ganga 929,055.
A bangaren condensates kuwa, rijiyoyin Agbami sun samar da ganga miliyan 2.01, Akpo ganga miliyan 1.34, yayin da Tulja-Okwuibome ya samar da ganga 304,827.
Rahoton ya nuna cewa yawan hakar mai ya rika sauyawa tsakanin ganga miliyan 1.46 zuwa miliyan 1.85 a rana cikin watan, amma matsakaicin watan Afrilu shi ne mafi girma da Najeriya ta samu a shekarar 2026 zuwa yanzu.
Hukumar ta danganta wannan ci gaba da ingantuwar ayyukan rijiyoyin mai, karin kwarewar gudanar da aiki, dawo da wasu rijiyoyin da suka samu matsala a baya, da kuma fara fitar da sabbin nau’ikan danyen mai kamar Cawthorne crude.
Jami’ai sun bayyana cewa wannan ci gaba na da alaka da gyare-gyaren da gwamnati ke yi domin kara gaskiya a bangaren mai, samar da kudaden musayar waje da kuma kara kudaden shiga ga gwamnatin tarayya.
Sai dai har yanzu akwai kalubale, domin wasu rahotanni sun nuna cewa Najeriya ta samar wa matatun cikin gida ganga miliyan 28.5 kacal a rubu’in farko na shekarar 2026, kasa da ganga miliyan 61.9 da aka ware domin su.
Duk da gibin da aka samu a farkon shekarar, karin yawan hakar mai a watan Afrilu ya nuna cewa bangaren man fetur na Najeriya na sake farfadowa, yayin da hukumomi ke nuna kwarin gwiwa cewa za a ci gaba da samun ci gaba duk da matsin lambar kasuwar duniya.
