Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals ta fitar da kimanin litar man fetur da sauran kayayyakin mai biliyan 1.66 zuwa kasashen waje a watan Afrilun 2026, kamar yadda sabon rahoton Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Tsakiya da Kasa ta Najeriya (NMDPRA) ya nuna.
Rahoton ya bayyana cewa kayayyakin da aka fitar sun hada da litar fetur miliyan 513, dizal miliyan 534 da kuma man jiragen sama miliyan 615. Wannan shi ne mafi girman adadin kayayyakin mai da matatar ta taba fitarwa cikin wata guda tun bayan fara aiki.
Ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da rikici tsakanin Amurka da Iran ke kara tsananta, tare da fargabar tangardar hanyoyin jigilar mai ta mashigin ruwa na Hormuz, wanda ke daya daga cikin muhimman hanyoyin safarar mai da iskar gas a duniya.
Masana harkar mai sun bayyana cewa rashin tabbas na siyasa a duniya ya kara bukatar samun wasu sabbin kasashen da za su rika samar da mai, lamarin da ke kara bai wa Najeriya damar zama cibiyar fitar da tataccen mai zuwa kasashen waje.
Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals mai karfin tace gangar danyen mai 650,000 a rana ita ce babbar matata mafi aiki a yanzu a Najeriya da ke samar da isasshen mai domin amfani cikin gida da kuma fitarwa zuwa kasashen waje.
Rahoton NMDPRA ya nuna cewa matatar ta yi aiki da kusan cikakken karfinta a watan Afrilu, yayin da matatun cikin gida suka karbi ganga miliyan 18.37 na danyen mai, idan aka kwatanta da ganga miliyan 13.11 a watan Maris.
Rahoton ya kara da cewa ana samar da matsakaicin litar fetur miliyan 53.6 a kullum, inda litar miliyan 40.7 ke shiga kasuwar cikin gida, yayin da litar miliyan 17.1 ke fita kasashen waje.
Haka kuma, samar da dizal ya kai matsakaicin litar miliyan 23.6 a rana, inda litar miliyan 17.8 daga ciki aka fitar zuwa kasashen waje.
A bangaren man jiragen sama kuwa, ana fitar da litar miliyan 20.5 a kullum, yayin da litar miliyan 2.6 kacal ake amfani da ita a cikin gida.
Karuwar fitar da man jiragen sama na zuwa ne makonni kadan bayan kamfanonin jiragen sama na Najeriya sun yi gargadin yiwuwar dakatar da ayyukansu saboda tashin farashin mai, lamarin da ke nuna muhimmiyar rawar da matatar Dangote ke takawa wajen tabbatar da wadatar mai.
Duk da karuwar tace mai a cikin gida, farashin fetur ya ci gaba da kasancewa mai tsada, yayin da farashin danyen mai ya kai matsakaicin dala 120.55 kan kowace ganga a watan Afrilu.
Masana tattalin arziki sun ce yawan kayayyakin da matatar Dangote ke fitarwa na nuna yadda Najeriya ke sauyawa daga kasar da ta dogara da shigo da tataccen mai zuwa kasar da ke fitar da shi zuwa kasashen duniya, yayin da rikice-rikicen duniya ke kara habaka bukatar man Najeriya.
