Ministan Kudi kuma Mai Kula da Tattalin Arzikin Najeriya, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba da dogaro da karbar bashi domin gudanar da ci gaba ba, yana mai jaddada bukatar gina tsarin kudi mai dorewa.
Oyedele ya bayyana hakan ne yayin taron shekara-shekara na 28 na Cibiyar Kwararrun Haraji ta Najeriya, inda ya ce dole ne kasar ta samar da tsarin kudaden shiga da zai iya tallafawa muhimman bangarori kamar gine-ginen more rayuwa, ilimi, lafiya, tsaro da shirye-shiryen jin kai ba tare da dogaro da bashi ba.
Ya ce: “Najeriya ba za ta ci gaba da daukar bashi domin gudanar da ci gaba ba. Dole ne mu gina tsarin kudi mai dorewa wanda zai iya tallafawa manyan ayyuka da bukatun jama’a.”
Ministan ya bayyana cewa gyaran harajin da gwamnati ke yi na da nufin saukaka tsarin haraji, rage yawan haraji iri-iri, tabbatar da adalci da kuma jawo hankalin masu zuba jari.
A cewarsa, gwamnati ta cire ma’aikatan da ke karbar mafi karancin albashi daga biyan harajin kudin shiga, yayin da aka rage nauyin haraji ga masu karamin da matsakaicin karfi.
Dangane da harajin kamfanoni, Oyedele ya ce gwamnati na shirin rage harajin kudin shiga na kamfanoni domin sanya Najeriya ta fi jan hankalin masu zuba jari daga ciki da wajen kasar.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati na sabunta tsarin harajin VAT ta hanyar fadada damar amfani da input credits da kuma fayyace kayayyakin da aka ware daga VAT domin rage matsin hauhawar farashi.
Ministan ya jaddada cewa fasaha za ta taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da haraji, inda gyare-gyaren za su mayar da hankali kan hada bayanai wuri guda, amfani da tsarin kwamfuta da kuma shigar da bayanan haraji ta yanar gizo.
Sai dai ya amince cewa akwai kalubale da suka hada da raunin hukumomi, yadda za a shigar da bangaren kasuwancin da ba a yi wa rajista ba cikin tsarin haraji, da kuma matsalar rashin amincewar jama’a.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, wanda mai ba shi shawara Tope Fasua ya wakilta, ya kare gyare-gyaren yana mai cewa suna da amfani ga jama’a da kasuwanci. Ya ce an tsara su ne domin fitar da miliyoyin ‘yan Najeriya daga talauci da kuma farfado da tattalin arzikin kasar.
Shugaban Cibiyar Haraji ta Najeriya, Innocent Ohagwa, ya bayyana gyare-gyaren a matsayin mafi girma cikin sama da shekaru 30.
Ya ce rabon kudaden shiga da ake kashewa wajen biyan basussuka ya ragu daga kashi 120 cikin 100 a shekarar 2022 zuwa kashi 68 cikin 100 a shekarar 2025.
A cewarsa, fadada masu biyan haraji zai taimaka wa Najeriya wajen “sauya daga kasar da ke rayuwa ta hanyar bashi zuwa kasar da ke zuba jari domin ci gaba.”
Sauran mahalarta taron da suka hada da Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, da Sanata Adams Oshiomhole, sun goyi bayan gyare-gyaren, suna masu cewa ya kamata attajiran Najeriya su rika bayar da gudunmawa mai yawa, tare da jaddada cewa haraji dole ne ya kasance ginshikin mulki da ci gaban kasa.
