Bankuna hudu a Najeriya — Access Bank, Union Bank of Nigeria, Stanbic IBTC Bank da Fidelity Bank — sun fitar da bayanan asusun ajiyar kudade guda 321,181 da aka dade ba a yi mu’amala da su ba, bayan umarnin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayar.
Matakin ya samo asali ne daga dokar da CBN ta fitar a watan Yulin 2024 kan asusun da suka yi dormancy da kudaden da ba a karba ba, wadda ta umurci bankuna su wallafa bayanan irin wadannan asusu watanni shida kafin a mayar da kudaden zuwa Asusun Amana na Kudaden da Ba a Karba ba na CBN.
Access Bank ta bayyana asusun dormant guda 243,934, inda adadin ya kusan daidaita tsakanin na mutane da na kamfanoni.
Fidelity Bank kuwa ta fitar da bayanan asusu 61,900, inda kusan kashi 79 cikin 100 na su na kamfanoni ne.
Haka kuma, Stanbic IBTC Bank ta wallafa asusu 26,135 a cikin shafuka 1,520, yayin da Union Bank of Nigeria ta fitar da jerin asusu 212 kacal, mafi yawansu na kungiyoyi, kungiyoyin hadin gwiwa da kungiyoyin jama’a ne.
Rahotanni sun nuna cewa asusun sun shafi kananan da matsakaitan sana’o’i, kamfanonin mai da iskar gas, masu harkar sufuri, coci-coci, makarantu da ‘yan kasuwa, musamman a Legas, Fatakwal da wasu cibiyoyin kasuwanci a Arewa.
Masana tattalin arziki sun nuna damuwa kan batun sirrin kwastomomi, hanyoyin sanarwa da kuma wahalar dawo da asusun dormant zuwa aiki.
Masanin tattalin arziki, Muda Yusuf, ya ce: “Abin da ya fi muhimmanci shi ne bankuna su rika sadarwa da kwastomominsu… sannan a saukaka hanyoyin dawo da asusun dormant aiki.”
Shi ma Farfesa Akpan Ekpo ya nuna shakku kan dalilin bayyana sunayen asusun a bainar jama’a, yana mai gargadin cewa hakan na iya jefa masu asusun cikin matsala ba tare da bukata ba.
Tsohon shugaban kungiyar kasuwanci ta Lagos Chamber of Commerce and Industry (LCCI), Gabriel Idahosa, ya ce yawan kudaden da ake bari a asusu na faruwa ne sakamakon rugujewar kasuwanci, mutuwar masu asusu ko kuma hadewar bankuna, yana mai cewa wallafa bayanan na iya janyo rikice-rikicen shari’a.
Sai dai CBN ta kare matakin, tana cewa kudaden da aka bari a dormant accounts na iya fuskantar damfara da cin zarafi.
Bankin ya bayyana cewa asusun da dokar ta shafa sun hada da na ajiya, current account, asusun kudaden waje, walat din prepaid, albashin da ba a karba ba, cheque da suka dade ba a cire ba, da sauran kadarorin kudi da ba a yi mu’amala da su ba tsawon akalla shekaru 10.
CBN ta kuma umurci bankuna su rika sanar da kwastomomi akai-akai ta hanyar imel, sakonnin waya da wasiku, tare da adana bayanan bincike da kuma gabatar da rahoton kwata-kwata domin kara inganta sa ido da bin ka’ida.
