Trends

Satar Wutar Lantarki Ta Jawo Asarar Naira Biliyan 111 Cikin Shekara 12 – GenCos

Kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya (GenCos) sun bukaci Gwamnatin Tarayya da kuma Hukumar Tsaron Tsarin Wutar Lantarki ta Kasa, wato NISO, da su bayyana sunayen kamfanoni da mutane da ake zargi da satar wutar lantarki tare da katse musu wuta da gurfanar da su a gaban kotu.

Bukatar ta biyo bayan bayyanar da NISO ta yi cewa wasu manyan kwastomomi na satar kusan megawatt 180 na wutar lantarki a jihohin Legas da Ogun ta hanyar kauce wa mita da kuma yin magudi da na’urorin aunawa.

Manajan Daraktan NISO, Abdu Mohammed Bello, ya bayyana satar wutar a matsayin abin mamaki matuka, yana mai cewa hakan na barazana ga daidaiton tsarin wutar lantarki da kuma kudaden shiga na kasuwar lantarki.

Ya ce binciken da aka gudanar ya gano cewa ana samun irin wadannan laifuffuka sosai daga manyan masu amfani da lantarki da ke da alaka da kamfanonin rarraba wuta na Ikeja da Ibadan DisCos.

Shugabar GenCos, Joy Ogaji, ta bayyana cewa kudin wutar da ake sata ya kai naira biliyan 9.7 a kowane wata, wanda ya haura naira biliyan 111 cikin shekaru 12. Ta ce masu zuba jari a bangaren lantarki na cikin mawuyacin hali yayin da “wasu ke more rayuwa da kudin da ba nasu ba.”

Ogaji ta jaddada cewa dole ne a sanya wadanda aka kama da hannu cikin jerin bakar fata, a gurfanar da su a kotu tare da tilasta musu mayar da kudaden da suka sata tare da kudin ruwa.

Masu ruwa da tsaki a bangaren lantarki sun nuna damuwa kan lamarin, suna cewa bai kamata a yi biris da shi ba.

Masana sun bayyana cewa satar lantarki da manyan kamfanoni ke yi ta fi illa sosai idan aka kwatanta da magudin mita da gidaje ke yi, tare da kira ga hukumomi da su mayar da hankali kan “manyan barayin lantarki.”

Domin dakile asarar kudaden shiga, NISO ta umarci a kara tsaurara bin dokokin amfani da wutar lantarki, sake daidaita mita, da kuma girka na’urorin duba wuta da na’urorin sauya wuta a duk wuraren hada tsarin lantarki.

Bello ya gargadi masu karya doka cewa za su fuskanci tara, biyan kudin wutar da suka sata, katse musu wuta ko ma dakatar da su daga kasuwar lantarki baki daya.

Ya kara da cewa NISO za ta hada gwiwa da Kamfanin Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) da jami’an tsaro domin kafa rundunar hadin gwiwa da za ta rika sa ido kan layin Ikorodu–Sagamu tare da tabbatar da bin doka. Ya ce za a fara aikin ne a matsayin gwaji kafin fadada shi zuwa sassan kasar baki daya.

Masana harkar lantarki sun ce dakile satar wutar lantarki na da matukar muhimmanci wajen farfado da bangaren wutar lantarki a Najeriya, inda rashin biyan kudin amfani da wuta ke ci gaba da hana samun zuba jari da inganta ayyuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *