Trends

NNPC, NUPRC Sun Tura N322bn da $116.9m ga FAAC

Kamfanin Man Fetur na Kasa, Nigerian National Petroleum Company Limited, da Hukumar Kula da Hako Danyen Mai ta Najeriya, Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission, sun tura sama da Naira biliyan 322 da dala miliyan 116.9 zuwa Asusun Tarayya (Federation Account) cikin watanni biyu kacal bayan fara aiwatar da Dokar Zartarwa ta 9 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa hannu a watan Fabrairun 2026.

Dokar ta umurci cikakken tura kudaden shiga daga danyen mai da iskar gas zuwa Asusun Tarayya domin kara gaskiya da kuma bunkasa kudaden shiga a lokacin da gwamnati ke fuskantar matsin tattalin arziki.

Tinubu ya ce, “Tsawon lokaci ana fama da yawan cire-cire, maimaita asusu, da matsalolin tsarin bangaren mai da gas da suka rage kudaden shiga… dole hakan ya tsaya.”

Takardun FAAC sun nuna cewa daga kudaden watan Maris 2026 da aka raba a watan Afrilu, NNPC ta tura dala miliyan 29.28 da Naira biliyan 42.64. Haka kuma daga kudaden watan Fabrairu da aka raba a watan Maris, kamfanin ya tura dala miliyan 87.63 da Naira biliyan 121.34.

Rahoton ya nuna cewa kudaden watan Maris sun hada da dala miliyan 25.7 daga fitar da danyen mai zuwa kasashen waje, dala miliyan 3.52 daga ribar kwangilolin PSC, da kuma Naira biliyan 37.67 daga kudaden danyen mai, baya ga kudaden gas da sauran hanyoyin samun kudin shiga.

An raba ribar PSC ne da tsarin kaso 60 zuwa 40 tsakanin Federation Sub-Account da Federation Account.

A nata bangaren, NUPRC ta tura Naira biliyan 34.2 a watan Maris daga kudaden royalty, tara kan konewar gas, kudin hayar wuraren hakar mai da sauran kudaden shiga na bangaren mai.

Sai dai adadin ya ragu sosai idan aka kwatanta da Naira biliyan 124.4 da aka tara a watan Fabrairu, sakamakon raguwar kudaden royalty.

Masana sun ce wadannan kudade na nuna kokarin gwamnati wajen kara gaskiya da rage almundahana a bangaren mai da gas.

Bankin Duniya ya bukaci gwamnati ta kara tsaurara aiwatar da Dokar Zartarwa ta 9, ciki har da dakatar da cire kudade kai tsaye daga tushe da kuma tabbatar da hukumomin gwamnati suna amfani da tsarin kasafin kudi mai gaskiya.

Jami’ai sun bayyana cewa wannan tsari zai kara yawan kudaden da ake rabawa gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi a kowane wata, domin taimaka wa jihohi wajen magance matsalar bashi, biyan albashi da gibin ababen more rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *