Farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya haura zuwa dala 104 kan kowace ganga a ranar Litinin, bayan da tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran ta rushe, lamarin da ya kara tayar da hankalin yiwuwar sabon rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta “na dab da mutuwa” bayan ya yi watsi da martanin da Tehran ta bayar kan sabon tayin Amurka.
Da yake magana da manema labarai, Trump ya ce, “A yanzu wannan shi ne mafi rauni, bayan karanta wannan shara da suka aiko mana. Ban ma gama karantawa ba.”
Rahotanni sun ce Iran ta bukaci a biya diyya kan barnar da yakin ya jawo, a amince da ikon ta kan mashigar ruwan Strait of Hormuz, a kawo karshen killacewar jiragen ruwa da Amurka ke yi, a dage takunkumin tattalin arziki, tare da cire takunkumin sayar da danyen man Iran.
Tayin Amurka kuwa ya fi mayar da hankali ne kan dakatar da fada kafin a tattauna batutuwa masu sarkakiya, ciki har da shirin nukiliyar Iran.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya kare matsayar kasarsa inda ya ce, “Bukatar mu halastacciya ce… tabbatar da zirga-zirga cikin aminci ta mashigar Strait of Hormuz da samar da tsaro a yankin da Lebanon na daga cikin bukatun Iran, kuma wannan tayi ne mai nuna alhaki da karamci.”
Rikicin ya sanya mashigar Strait of Hormuz cikin matsin lamba mai tsanani. Mashigar ruwan, wadda ke daukar kusan kashi 20 cikin 100 na jigilar danyen mai da iskar LNG ta duniya, ta zama cibiyar rikici tun bayan barkewar yaki a ranar 28 ga Fabrairu, lokacin da farashin mai bai kai dala 70 ba kan kowace ganga.
Bayanan harkokin sufuri sun nuna cewa jiragen dakon mai na kara kashe na’urorin bibiyar tafiyarsu domin kaucewa hare-haren Iran. A ranar Lahadi, manyan jiragen dakon mai guda biyu — Agios Fanourios I da Kiara M — dauke da gangar mai miliyan biyu kowannensu na danyen man Iraki sun ratsa mashigar ruwan.
Jirgin Agios Fanourios I, wanda ke kan hanyarsa zuwa Matatar Mai ta Nghi Son da ke Vietnam, ya kasa ketare mashigar sau biyu tun bayan loda man Basrah a watan Afrilu, abin da ke nuna irin hadarin da ke barazana ga samar da makamashi a duniya.
Masana tattalin arziki sun gargadi cewa ci gaba da wannan tangarda ka iya tsawaita tashin hankalin kasuwar makamashi, yayin da farashin danyen mai na Brent ya karu da kashi 2.7 cikin 100 a ranar Litinin sakamakon fargabar karin tangardar samar da mai.
