Trends

Najeriya Ta Fitar da Gangar Danyen Mai Miliyan 485 a 2025

Hukumar Kula da Masana’antar Hako Danyen Mai ta Najeriya (NUPRC) ta bayyana cewa Najeriya ta fitar da gangar danyen mai miliyan 485.44 zuwa kasuwannin ƙetare a shekarar 2025, adadin da ya kai kashi 82 cikin 100 na jimillar man da aka samar a shekarar.

Rahoton hukumar ya nuna cewa ƙasar ta samar da jimillar gangar mai miliyan 592 a shekarar da ta gabata, wanda ya yi daidai da matsakaicin gangar mai miliyan 1.62 a kullum.

Daga cikin wannan adadi, an fitar da gangar mai miliyan 1.33 a kullum zuwa ƙasashen waje, yayin da gangar mai dubu 290 a kullum, wato kashi 18 cikin 100, aka ware domin matatun mai na cikin gida.

Rahoton ya ce tsarin samar da man ya ci gaba da kasancewa iri ɗaya, inda danyen mai ya wakilci kashi 82 cikin 100, yayin da condensates suka kasance kashi 18 cikin 100. Hukumar ta bayyana hakan a matsayin “daidaitaccen tsarin albarkatun hydrocarbons na Najeriya.”

Hukumar ta kuma bayyana cewa yawan man da aka ɗora domin fitarwa ya yi daidai da yawan man da aka samar, lamarin da ke nuna ingantuwar ayyuka da kuma tsarin lissafi a bangaren mai. Sai dai rahoton ya nuna cewa yawan dogaro da fitar da mai zuwa ƙasashen waje na nuna yadda tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da jingina da kasuwannin duniya, tare da fuskantar barazanar sauyin farashin mai a kasuwar duniya.

A bangaren matatun mai na cikin gida kuwa, rahoton ya ce ana ci gaba da ware wani kaso na danyen mai domin tallafa wa bunkasar tace mai a cikin gida da rage dogaro da shigo da man fetur daga waje.

NUPRC ta ce yadda bangaren zai kasance a gaba zai dogara ne da matakan kungiyar OPEC, yanayin bukatar mai a duniya, da kuma daidaita ayyukan matatun mai na cikin gida.

Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da Matatar Mai ta Dangote ke fama da karancin danyen mai. Tsakanin watan Oktoban 2025 zuwa tsakiyar watan Maris 2026, matatar ta samu gangar mai miliyan 29.21 kacal, kasa sosai idan aka kwatanta da gangar mai miliyan 108.74 da ake bukata domin gudanar da aiki yadda ya kamata. Wannan na nuna cewa matatar ta samu kashi 26.9 cikin 100 ne kawai na bukatarta.

Rukunin Kamfanin Dangote ya koka da cewa wasu kamfanonin hako mai na cikin gida na kin samar musu da danyen mai yadda ya kamata, lamarin da ya tilasta musu dogaro da shigo da mai daga kasashen waje.

Kamfanin ya ce, “Muna karɓar kusan lodin mai guda biyar a wata daga NNPC, wanda muke biya da naira, amma hakan bai kai lodin guda 13 da ake bukata ba.”

Masu ruwa da tsaki a bangaren tace mai, ciki har da kungiyar CORAN, sun bukaci a kara samar da danyen mai ga matatun cikin gida, suna mai cewa samun wadataccen danyen mai na da muhimmanci wajen tabbatar da ribar matatun mai da kuma tsaron makamashin kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *