Trends

Museveni Mai Shekaru 81 Ya Fara Sabon Wa’adi a Matsayin Shugaban Uganda

Shugaban ƙasar Uganda, Yoweri Museveni, ya rantsar da kansa domin fara wa’adinsa na bakwai bayan shafe kusan shekaru 40 yana mulkin ƙasar Gabashin Afirka.

Museveni, mai shekaru 81, ya ci gaba da zama shugaban ƙasar ne a jere na karo na bakwai, wanda zai ƙara masa wani wa’adi na shekaru biyar a kan mulki.

An rantsar da shi a ranar Talata a yankin Kololo da ke birnin Kampala, inda dubban mutane suka halarci bikin tare da taya shi murna yayin da ya karɓi kayan mulki na gargajiya.

A jawabinsa, Museveni ya yi kira ga ‘yan Uganda da su dage wajen aiki tukuru da kuma gina arziki ga iyalansu, yana mai misalta labaran wasu mutane da suka samu nasara ta hanyar kasuwanci. Ya ce: “Babu sauran uzuri.”

Rahotanni sun nuna cewa yawancin ‘yan Uganda sun fara ganin cewa mulkin Museveni, wanda shi ne kaɗai shugaba da yawancinsu suka taɓa sani, yana dab da ƙarewa.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da yadda sauyin shugabanci zai kasance ba, da kuma yadda za a gudanar da mika mulki cikin tsari a lokacin da zai bar ofis.

Shugaban rundunar sojin ƙasar, Janar Muhoozi Kainerugaba, wanda shi ne ɗan shugaban ƙasar kuma ake ganin zai iya gaje shi, ya jagoranci shirye-shiryen faretin soji na kwanaki da dama.

Bikin rantsarwar ya kasance mai armashi, inda jiragen yaƙi na Rasha samfurin Sukhoi suka rika shawagi a sararin samaniyar Kampala, babban birnin Uganda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *