Farfesa Muhammad Sani Bello, wanda aka fi sani da Mainan Zazzau, ya ajiye mukaminsa na Kwamishinan Yada Labarai kuma mamba a Majalisar Zartaswar Jihar Kaduna.
A cikin wata wasika da ya aike wa Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Bello ya bayyana cewa murabus ɗinsa zai fara aiki daga ranar 29 ga Yuli, 2025.
Ya tunatar da cewa an nada shi ne a hukumance a ranar 27 ga Yuli, 2023, bisa wasiƙar da ta ɗauki lamba GHIKDISI171, a matsayin kwamishina a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Uba Sani.
Farfesa Bello ya fara aikin kwamishinanci ne a Ma’aikatar Ilimi, inda ya yi aiki har zuwa watan Mayu 2025, kafin a mayar da shi zuwa sabuwar Ma’aikatar Yada Labarai da aka dawo da ita a hukumance.
An ba shi alhakin jagorantar kafa da kuma fara aiwatar da ayyukan ma’aikatar tun daga tushe.
Farfesa Bello ƙwararren masani ne a fannin lissafin kuɗi da kasuwanci, kuma ya samu gogewa mai yawa a banki, kula da harkokin kuɗi, ilimi da kuma aikin gwamnati.



