Ƙasar Maroko ta shigar da ƙara zuwa hukumar kwallon ƙafa ta nahiyar Afrika (CAF), tana ƙalubalantar shigar’yan wasan Najeriya biyu a wasan karshe na gasar WAFCON, wanda Super Falcons ta lashe da ci 3-2 a ranar 26 ga Yuli.
A baya dai, Maroko ce ta karɓi bakuncin gasar, kuma a wasan karshe ta tafi hutun rabin lokaci tana jan ragamar wasa da ci 2-0, sai dai tawagar Super Falcons ta dawo da karfi a zagaye na biyu, inda ta ci kwallaye uku da suka bata nasara da kuma kambin zakara karo na goma a tarihin ta.
Kafin wasan karshe, Maroko ta shigar da koke akan halascin ‘yan wasan Najeriya biyu: Ashleigh Plumptre da Michelle Alozie. Dukansu an haife su ne a ƙasashen waje amma suka zaɓi wakiltar Najeriya a matakin manyan ‘yan wasa.
A cikin ƙarar da suka shigar, Maroko ta bayyana cewa akwai matsala wajen yadda ‘yan wasan suka sauya ƙasarsu zuwa Najeriya, tana zargin cewa akwai rashin daidaito da ya kamata a bincika dangane da ikirarin da suka yi na kasancewa ‘yan Najeriya.
Maroko na fatan a soke nasarar Najeriya bisa dalilin amfani da waɗannan ‘yan wasa a cikin gasar.
Plumptre dai ta samu amincewar FIFA tun a shekarar 2021 domin wakiltar Najeriya, bayan an tabbatar da cewa kakanta na bang



