Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin DCG Olumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kula da Gobara ta Ƙasa (Federal Fire Service – FFS), wanda zai fara aiki daga ranar 14 ga Agusta, 2025.
Sanarwar nadin ta fito ne daga Hukumar Kula da Tsaro ta Gida, Gyaran Hali, Gobara da Shige da Fice (CDCFIB), wadda Sakataren hukumar, Abdulmalik Jibrin, ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta bayyana cewa:
“Wannan nadin ya biyo bayan shirin ritayar Shugaban Hukumar mai ci yanzu, Injiniya Abdulganiyu Jaji Olola, wanda zai yi ritaya a ranar 1 ga Agusta, 2025, bayan cika shekaru 60.”
DCG Olumode Samuel Adeyemi dai yana da gagarumar ƙwarewa a aikin gobara, inda ya fara aikinsa daga Hukumar Kula da Gobara ta Babban Birnin Tarayya (FCT), kafin a mayar da shi zuwa Hukumar Gobara ta Ƙasa, har ya kai matsayin Mataimakin Shugaban Hukumar (Deputy Controller-General) a sashen kula da albarkatun mutane a hedkwatar hukumar.
A tsawon aikinsa, ya halarta tare da kammala dukkan horo da ake bukata ga ma’aikatan hukumar, ciki har da horo na jagoranci da wasu ƙarin kwasa-kwasai a cikin gida da ƙetare.
Ya rike muƙamai daban-daban a hukumar, kuma memba ne/kwararre a cikin kungiyoyin ƙwararru kamar haka: Association of National Accountants of Nigeria (ANAN), Institute of Corporate Administration of Nigeria, Institute of Public Administration of Nigeria, da Chartered Institute of Treasury Management of Nigeria.
Hukumar CDCFIB ta nuna godiyarta ga Shugaban Hukumar mai ritaya, Injiniya Abdulganiyu Jaji Olola, bisa irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban Hukumar Gobara ta Ƙasa, tare da yabawa da kishinsa da jajircewarsa, da kuma muhimman sauye-sauyen da ya jagoranta a lokacin da yake kan kujerar shugabanci.



