Binciken NNPCL: Bayo Ojulari, Ya Roki Majalisar Dattawa Da Ta Ba Shi Lokaci

Shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Bayo Ojulari, ya roƙi Majalisar Dattawa da ta ba shi ƙarin lokaci domin gudanar da cikakken bincike kan bambancin kuɗi da ya kai Naira tiriliyan 210 da ke cikin asusun kamfanin.

Ojulari ya bayyana hakan ne a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lissafin Kudin Jama’a (Public Accounts Committee) a ranar Litinin, 29 ga Yuli, inda ya nemi ƙarin lokaci don nazari da daidaita matsalolin da aka gano a cikin takardun lissafin kudin da aka yi wa NNPCL daga shekarar 2017 zuwa 2023.

“Ina da kusan kwana 100 kacal a ofis, kuma ina bukatar lokaci don fahimtar matsalolin sosai. Dangane da bayani da na samu yau, ra’ayina ya sauya. Ina bukatar ci gaba da bincike da daidaito na cikin gida domin kawo amsoshin da kwamitin ke bukata,” in ji Ojulari.

Shugaban NNPCL ya tabbatar wa da ‘yan majalisar dattawa cewa zai kafa tawaga ta musamman don duba tambayoyin da kwamitin ya gabatar.

Kwamitin ya nuna damuwa kan bashin da ya kai Naira tiriliyan 103 da kadarori da suka kai Naira tiriliyan 107, yana bayyana cewa wadannan alkaluman suna da rikitarwa kuma ba su da tabbaci.

Shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wadada, ya bayyana cewa: “Adadin yana da matukar girma. Ba za a iya tabbatar da adadin bashin ba, don haka ba za mu karɓa ba. Haka kuma, kudaden da ake karɓa a matsayin kadarori ba su da ingantaccen tushe.”

Ya ce wannan Naira tiriliyan 210 da ake tambaya na cikin takardun da aka tantance daga asusun kamfanin, kuma ya bukaci a samar da cikakken bayani dangane da bashin da kadarorin da aka nuna.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar sun soki yadda NNPCL ke tunkarar batun, suna zargin kamfanin da nuna rashin kulawa ga ikon sa-ido na kwamitin.

Sun kuma tambayi dalilin da yasa Shugaban Kamfanin bai da cikakken masaniya kan muhimman bayanan kuɗi, duk da cewa ya tura wakilai zuwa zaman kwamitin a baya.

Biyo bayan roƙon Ojulari, kwamitin ya amince da ba NNPCL wa’adin kwana 21 don dawo da cikakken bayani da daidaitattun amsoshi kan bambancin kuɗin.

Wannan ci gaba ya nuna yadda ake ƙara matsa lamba wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin kuɗi na kamfanin mai mallakin gwamnati, wanda aka sake fasalta shi zuwa kamfani mai iyaka (limited liability company) a shekarar 2022.