Kwamishinan Harkokin Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye mukaminsa sa’o’i bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ke nazarin rawar da ya taka a batun bayar da beli ga wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Wannan mataki na murabus ana kallonsa a matsayin wani muhimmin cigaba da ke kara tabbatar da jajircewar gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen tabbatar da gaskiya, rikon amana da daukaka matsayin shugabanci mai tsafta.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Alhaji Namadi ya bayyana cewa ya yanke shawarar murabus ne saboda bukatar kare martabar gwamnati da kuma la’akari da yadda al’amari ya ke da matukar sarkakiya da tasiri.
“A matsayina na dan wannan gwamnati da ke gaba da gaba wajen yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi, dole ne na dauki wannan mataki – ko da yake yana da ciwo,” inji shi.
“Duk da cewa ina ci gaba da nacewa ban aikata wani laifi ba, ba zan iya yin watsi da yadda jama’a ke kallon al’amarin da kuma bukatar kare darajojin da muka gina tare ba.”
Alhaji Namadi ya mika godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba shi na yi wa jihar hidima, tare da tabbatar da cewa yana nan daram wajen goyon bayan akidar kyakkyawan shugabanci da gaskiya.
“A matsayina na dan kasa nagari, dole ne in kare, in kiyaye, kuma in ci gaba da riko da amana da burin da muka aza wa jiharmu. Har ila yau, ina nan da biyayya ga manufofin da suka kafa wannan gwamnati,” inji shi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din Kwamishinan tare da yi masa fatan alheri a sauran rayuwarsa. Haka kuma, gwamnan ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da adalci, ladabi da yaki da safarar miyagun kwayoyi da sauran munanan dabi’u da ke barazana ga matasa da al’umma gaba ɗaya.
Gwamna ya kuma ja hankalin dukkan masu rike da mukaman siyasa da su rika yin taka-tsantsan a kan duk wata magana da ta shafi al’umma, tare da neman izini daga manyan hukumomi kafin shiga cikin lamura masu sarkakiya ko na siyasa.


