Trends

Ambaliya: Ribadu da Mustapha Sun Taimaka wa Mutane 500 a Jihar Adamawa da Kayan Agaji

Boss Mustapha tare NSA Nuhu Ribadu

Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Mallam Nuhu Ribadu, tare da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa (Arewa maso Gabas), Kwamared Salihu Mustapha, sun raba kayan tallafi ga sama da mutane 500 da ambaliya ta shafa a karamar hukumar Yola ta Kudu da ke Jihar Adamawa.

Wannan matakin na zuwa ne kwanaki uku bayan da mutane sama da iyalai 700 da ambaliya ta shafa suka karɓi irin wannan tallafi daga wadannan shugabannin biyu.

Yayin rabon kayan a karshen mako, Sakataren Shirye-shiryen Jam’iyyar APC na Jihar Adamawa, Kwamared Mustapha Atiku Ribadu, wanda ya wakilci shugabannin, ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin jajircewar su wajen tallafa wa al’ummomin da ambaliya ta shafa.

“NSA yana cikin damuwa matuka da halin da wadanda ambaliya ta shafa suke ciki. Wannan zagaye na biyu ya nufi mutane 500, kuma akwai wasu karin matakai da ake shiryawa don taimaka wa iyalai su koma rayuwa mai kyau,” inji shi.

Ya bayyana cewa akwai shirye-shiryen taimaka wa wadanda gidajensu suka rushe ko suka zama marasa amfani sakamakon ambaliyar.

A cikin kayan tallafin da aka raba sun hada da barguna, tabarmi, kayan yara da sauran muhimman kayayyaki da za su taimaka wajen saukaka rayuwa

Ribadu ya bayyana cewa kwamitin hadin gwiwa da ya kunshi shugabannin jam’iyya, wakilan al’umma da shugabannin addinai sun gudanar da bincike da tantance wadanda ambaliyar ta shafa kafin a fitar da sunayensu a matsayin wadanda suka cancanci tallafi.

Ya kara da cewa an yi shirye-shirye na musamman don kai wa masu rauni da tsofaffi da marasa lafiya wadanda ba za su iya zuwa wuraren rabon kayan ba.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin sun bayyana godiyarsu, tare da rokon gwamnati da sauran ‘yan Najeriya masu hannu da shuni da su ci gaba da taimaka musu wajen sake farfado da rayuwarsu.