Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gargadi jam’iyyun siyasa da su guji fara yakin neman zabe da wuri domin zaben 2027, tana mai bayyana hakan a matsayin karya dokar zabe.
Mai magana da yawun shugaban INEC, Mista Rotimi Oyekanmi, ne ya fitar da wannan gargadi a wata hira da aka yi da shi a Abuja, inda ya mayar da martani kan yadda ake ganin wasu jam’iyyu da ‘yan siyasa sun fara kamfen da wallafa hotunan takara kafin lokacin da doka ta tanada.
“Ina so in jaddada cewa INEC ba ta fitar da jadawalin shirye-shiryen zaben 2027 ba,” in ji Oyekanmi. “Saboda haka, babu wata jam’iyya da ta gudanar da zaben fidda gwani, kuma babu wanda aka tsayar da shi a matsayin dan takara har yanzu.”
Ya kara da cewa, “Sashe na 94 (1) na Dokar Zabe ta 2022 ya fayyace cewa yakin neman zabe a bainar jama’a daga jam’iyyu zai fara ne kwanaki 150 kafin ranar kada kuri’a kuma ya tsaya awanni 24 kafin ranar zabe.”
“Sashe na 95 (1) na dokar ya kuma bayyana cewa dan takara da jam’iyyarsa za su gudanar da yakin neman zabe ne bisa ka’idoji da sharuddan da INEC za ta tsara.”
Oyekanmi ya bayyana cewa duk da cewa ‘yan Najeriya suna da ‘yancin tattaunawa da bayyana ra’ayoyinsu kan babban zabe mai zuwa, kowane irin bude kamfen ko neman kuri’u a bainar jama’a tun yanzu na zaben 2027 ba daidai ba ne kuma ya saba wa doka.
Ya bayyana cewa an jaddada wannan matsayi ga dukkan jam’iyyun siyasa a taron tuntuba na karshe da hukumar INEC ta gudanar, inda ya ce ana sa ran za su bi doka cikin kashi dari.
INEC ta bukaci jam’iyyun siyasa su bi ka’ida wajen shirye-shiryensu na siyasa, tana mai cewa dole ne a mutunta dokar kasa domin tabbatar da daidaito da gaskiya a harkokin siyasa.
