Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya roki Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta farfado da kamfanin United Nigeria Textiles (UNTL) da ke Kaduna, yana mai cewa a halin yanzu akalla ayyukan yi 10,000 ne ke cikin hadari.
Sanusi ya yi wannan roko ne a ranar Talata, yayin da Ministan Harkokin Masana’antu na Jihohi, Sanata John Enoh, ya kai ziyara ta musamman tare da gudanar da taron tuntuba da masu ruwa da tsaki domin dawo da martabar bangaren masana’antar dinki, auduga da kayan sawa a Kaduna, kamar yadda wata sanarwa daga ma’aikatar ta bayyana.
Ziyarar na daga cikin kokarin Gwamnatin Tarayya karkashin tsarin farfado da masana’antu da ke cikin batu na 7 na tsare-tsaren Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya mayar da hankali kan samar da ayyukan yi, bunkasar tattalin arziki mai ratsa kowa da kowa da kuma ci gaban masana’antu.
Sarkin ya ce, “Rufe kamfanin UNTL tun daga shekarar 2022 abin damuwa ne matuka, musamman ganin cewa kamfanin yana da tarihi na daukar sama da ma’aikata 10,000 daga fannin sarrafa auduga zuwa dinki da kera tufafi.”
Ya kara da cewa, “Tasirin da rushewar UNTL ke da shi ga matasa da mata na da matukar hatsari ga zaman lafiya, musamman a Arewacin Najeriya.”
Don haka, Sanusi ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta shawo kan matsalolin da suka hada da rashin ingantaccen wutar lantarki wanda ke kawo tsaiko ga aikin masana’antu, yaduwar kayayyakin dinki da ake shigo da su ta barauniyar hanya wanda ke rage gasa da kamfanonin cikin gida, da kuma rashin tsauraran matakai na kare haƙƙin mallaka wanda ke hana kirkire-kirkire da zuba jari a bangaren.
Da yake mayar da martani, Sanata John Enoh ya amince da matsalolin da Sarkin ya gabatar, inda ya jaddada cewa karkashin jagorancin Shugaba Tinubu, gwamnati ta dauki matakai da dama don sake farfado da bangaren masana’antar.
Ya ce, “Wadannan matakai sun hada da shirya tarurruka da masu ruwa da tsaki don gano matsaloli da hanyoyin magance su, da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu, da hadin gwiwa da abokan ci gaba don karfafa manufofin da za su tallafa wa masana’antun cikin gida da habaka fitar da kaya zuwa kasashen waje.”
Enoh ya jaddada muhimmancin farfado da UNTL, yana mai cewa dawo da ayyukanta cikin cikakken aiki zai dawo da kwarin gwiwa kan tarihin masana’antar dinki a Najeriya da kuma hanzarta habakar masana’antu gaba daya.
