Fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, ya saki mutane 32 da ya yi garkuwa da su tare da daukar alkawarin daina kai hare-hare kan manoma, bayan tattaunawar zaman lafiya da aka yi da wasu malamai na addini.
Tattaunawar zaman lafiyar ta samu jagorancin fitaccen malamin addini, Sheikh Musa Yusuf (Asadus-Sunnah), wanda ya gana da Turji da sauran shugabannin ‘yan bindiga a sansaninsu da ke cikin karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.
Sheikh Yusuf ya bayyana cewa al’ummar Shinkafi ne suka roki malamai da su shiga cikin al’amarin domin samun damar komawa gonakinsu cikin kwanciyar hankali. An gudanar da ganawar ne sau uku a watan Yuli a cikin dajin Fakai.
“Ina tabbatar muku mun gana da Bello Turji, Dan Bakkolo, Black, Kanawa da Malam Ila. Jita-jitar cewa an kashe Dan Bakkolo ba gaskiya ba ce. Wadannan sune ke addabar yankin, kuma dukkansu sun amince da shawarwarin zaman lafiya, ciki har da mika wasu daga cikin makamansu domin nuna niyyar su ta gaskiya,” in ji Sheikh Yusuf.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun mika makamansu a matakai guda uku daban-daban, sannan suka ba wa manoman Shinkafi damar komawa gonakinsu ba tare da tsangwama ba. “Mun amince cewa dole ne a bar Fulani su shiga birane ba tare da ake musu kallon da bai dace ba ko kashe su ta hannun kungiyoyin sa-kai ba,” in ji shi.
Bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya, yankin Shinkafi ya fara samun zaman lafiya, inda manoma ke ci gaba da ayyukansu ba tare da tsoro ba. Sheikh Yusuf ya kuma ja kunnen sauran malamai da su guji fadin abubuwan da ka iya tayar da husuma, yana mai jaddada muhimmancin warware rikici ta hanyar sulhu da fahimta.
Ya jinjinawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mai Ba da Shawara kan Tsaro Nuhu Ribadu, Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, da Sanata Shehu Buba bisa goyon bayan da suka bai wa wannan shirin zaman lafiya. Ko da yake wannan yarjejeniya ba za ta kawo karshen ta’addanci gaba daya a jihar Zamfara ba, amma al’ummomin da ke karkashin ikon Bello Turji na cin moriyar zaman lafiya da kwanciyar hankali a halin yanzu.
