Zaben 2027: Tabbas Muna Tunanin Tsayar da Jonathan / Kwankwaso – Shugaban PDP

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa domin tsayar da tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben shekarar 2027.

Tun bayan rashin nasararsa a zaben 2015, Jonathan ya dan nesanta kansa daga harkokin siyasa. Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa jam’iyyar PDP na tattaunawa da shi domin ya dawo takara, tare da fatan kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben gaba.

Rahotanni da dama sun kuma bayyana cewa PDP na kokarin janyo tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya dawo cikin jam’iyyar tare da yiwuwar yin mataimaki ga Jonathan.

BBC ta ruwaito cewa wasu manyan shugabannin jam’iyyar, ciki har da gwamnoni, sun shiga tattaunawa domin lallaba Jonathan da Kwankwaso su amince da wannan tayin.

Masana siyasa na ganin wannan mataki na PDP na da nasaba da yunkurin rage karfin hadin guiwa tsakanin wasu jam’iyyu irin su African Democratic Congress (ADC).

Malam Ibrahim Abdullahi, mataimakin sakataren yada labarai na kasa na PDP, wanda ya halarci daya daga cikin tarukan tattaunawar, ya tabbatar wa BBC cewa Jonathan ya nuna sha’awar amsa kiran jam’iyyar.

A cewar Abdullahi, PDP na kokarin dawo da Jonathan ne bisa bukatar al’umma da ke ganin akwai bukatar komawarsa don gyara kura-kuran da aka tafka a baya.

“Lokacin da yake mulki, mutane na ganin kwarewarsa da salon jagorancinsa. Tun da har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP, muna ganin ya dace ya sake tsayawa takara. Yanzu jama’a sun gane cewa ba laifinsa kadai bane abubuwan da suka faru a baya. Suna neman gafararsa tare da fatan dawowarsa. Shi mutum ne mai tausayi,” in ji Abdullahi.

“Domin mu masu biyayya ne ga muradun ‘yan Najeriya, mun saurari kiraye-kirayensu, kuma muna daukar matakai a wannan hanyar.”

Rahotanni sun nuna cewa wasu jiga-jigan PDP sun gana da Jonathan a kasar Gambiya a makon da ya gabata a wani yunkuri na karshe don shawo kansa ya tsaya takara a zaben shugaban kasa na 2027.

Sai dai, an bayyana cewa Jonathan ya gindaya wasu sharudda kafin amincewa da dawowar tasa cikin tsaka-tsakin siyasa.

Daya daga cikin sharuddan da Jonathan ya gabatar, a cewar Abdullahi, shine a fayyace masa ko zai tsaya takara a zaben fidda gwani na jam’iyyar ko kuwa za a tsayar da shi a matsayin dan takara na hadin kai.

Ana kuma cewa tsohon shugaban yana tuntubar aminansa da na kusa da shi kafin ya yanke hukunci na karshe.

Tun daga zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, mutane da dama – musamman daga Arewacin Najeriya – ke ci gaba da kiran Jonathan ya dawo, suna danganta matsin rayuwar da ake fuskanta da mulkin da ya biyo bayansa.

Wasu na kallon Jonathan a matsayin shugaba mai sassaucin hali da hankali, wanda ya fi yin taka-tsantsan fiye da wadanda suka biyo bayansa.

Masana na ganin sha’awar PDP kan Jonathan ba ta rasa nasaba da tsarin karba-karba na mulki, inda ake sa ran shugaban kasa zai koma Kudu a zaben 2027.

Farfesa Abubakar Kari daga Jami’ar Abuja ya bayyana cewa idan Jonathan ya amince ya tsaya takara tare da samun goyon bayan jam’iyya ba tare da hamayya ba, kuma aka hada shi da dan takara daga Arewacin Najeriya, hakan zai canza taswirar siyasar 2027 matuka.

“Ina ganin idan Jonathan ya tsaya takara, zai farfado da PDP da ta dade tana cikin kunci. Takararsa na iya rushe wasu hadin kan jam’iyyun adawa da ke ganin kansu a matsayin ginshikin adawa,” in ji Farfesa Kari.

“Salon natsuwarsa da kuma yadda ya amince da sakamakon zabe tare da mika mulki cikin lumana a 2015 sun kara masa kwarjini a idon jama’a.”

Ya kara da cewa wata fa’ida da ke goyon bayan Jonathan ita ce iyakancewar mulkinsa zuwa wa’adi daya kawai bisa tsarin kundin tsarin mulki, wanda ke iya karawa Arewa kwarin guiwar cewa mulki zai dawo gare su bayan wa’adinsa.