Tsoffin Sojojin Isra’ila Sun Nemi Trump Ya Matsawa Netanyahu Don Kawo ƙarshen Yaƙin Gaza.
Tsaffin jami’an tsaron na Isra’ila sun bayyana buƙatar tasu ce cikin buɗaɗɗiyar wasiƙar da suka aika wa shugaban na Amurka, inda suka bayyana cewa dogon nazarin da suka yi a matsayinsu na ƙwararru kan sha’anin tsaro, ya basu damar samun tabbacin cewar, a halin yanzu ƙungiyar Hamas ba ta tattare da wata barazana ga Isra’ila….

