Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Katsina ta nada tsohon Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, a matsayin sabon hakimin gargajiya duk da cewa yana fuskantar shari’a kan zargin zambar makudan kudade da dama.
An nada Hadi Sirika a matsayin Marusan Katsina, wato Hakimin Gundumar Shargalle da ke karamar hukumar Dutsi a Jihar Katsina.
Sirika, wanda ya yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari, na fuskantar shari’a bayan da hukumar EFCC ta kammala bincike a kansa bayan barin ofis a shekarar 2023.
EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotuna biyu daban-daban bisa zargin karkatar da kudade da kuma amfani da mukaminsa wajen fifita kamfani mai suna Al Buraq Global Investment Limited, wanda aka ce yana da alaka da ‘yarsa da mijinta.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa hakan ya sabawa sashi na 12 na dokar ICPC – wato dokar hana cin hanci da rashawa da aikata laifuka makamantansu.
Baya ga nadin Sirika, majalisar ta kuma nada Umar Dikko Radda, ɗan Gwamna Dikko Radda, a matsayin Gwagwaren Katsina, wato Hakimin Gundumar Radda da ke cikin Karamar Hukumar Charanchi.
Wadannan nadin sarautu sun janyo cece-kuce a tsakanin al’umma, musamman duba da cewa daya daga cikin wadanda aka nada na fuskantar shari’a kan zarge-zargen cin hanci da rashawa.



