Gwamnatin Jihar Gombe ta kaddamar da sabuwar tasha mai karfin 620KW da ke kunshe da hada-hadar karamin karfi na ruwa (hydropower) da kuma hasken rana (solar PV hybrid system) a Dam din Balanga da ke Talasse, cikin Karamar Hukumar Balanga ta jihar.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda mataimakinsa, Dr Manassah Daniel Jatau, ya wakilta, ya bayyana wannan aiki a matsayin babban ci gaba wajen samar da wutar lantarki, raya karkara da kuma bunkasa masana’antu a jihar.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce wannan aikin na daya daga cikin muhimman manufofin gwamnatinsa na ci gaban ababen more rayuwa, karfafa tattalin arziki da kuma kare muhalli.
Ya kara da cewa:
“Wannan aiki ya zo a kan kari kuma yana da matukar amfani. Ya dace da burinmu na dogaro da kai, dorewa da ci gaba mai inganci ga kowa da kowa. Wutar lantarki ginshiki ce ta ci gaban zamani. Wannan tsarin zai canja rayuwa, ya inganta aikin gona, samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwar al’umma a Balanga da kewaye.”
Rahotanni sun nuna cewa aikin yana karkashin tallafin Tarayyar Turai (EU), Asusun Muhalli na Duniya (GEF), da Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Samar da Wuta a Karkara (REA), tare da hadin gwiwar Kungiyar Raya Masana’antu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIDO).
Wannan tsarin na hadaka yana amfani da karamin karfin ruwa da kuma hasken rana domin samar da wutar lantarki mai dorewa, tare da niyyar bunkasa sana’o’in cikin gida, kara ingancin rayuwa da kuma cika kudirin kasa na samar



