Category: Business
Business
Jirgin Ƙasa: Abuja–Kaduna Zai Fara Aiki Nan da Mako – NRC
Hukumar Jiragen Ƙasa ta Ƙasa (NRC) ta sanar a ranar Asabar cewa sabis na jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna zai koma aiki nan da mako mai zuwa. Wannan ya biyo bayan kammala gyare-gyare da binciken tsaro a ɓangaren layin da aka lalace. A tunawa, an dakatar da aikin jirgin ne bayan hatsarin da ya…
Za a Fara Samun Fasfo a Cikin Kwana 7 – Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa nan ba da jimawa ba za su rika samun fasfo dinsu cikin kwanaki bakwai kacal bayan kammala aikace-aikace. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana haka, inda ya ce hakan zai yiwu ne sakamakon inganta kayan aikin Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS). Da…
Botswana ta Nada Dan Nigeriya a Matsayin Shugaban Sabon Asusun Ajiya
Shugaban ƙasar Botswana, Advocate Duma Gideon Boko, ya naɗa Farouk Gumel, ɗan Najeriya kuma Mataimakin Shugaban Tropical General Investment (TGI) Group a Afrika, a matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Botswana Sovereign Wealth Fund Limited (BSWF). An ƙaddamar da asusun a Gaborone An sanar da wannan naɗi ne a wajen ƙaddamar da sabon asusun ajiya na…
Shugabancin Zone A: ACG Babandede ya Karba Karaga Daga Orbih
Mataimakin Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya (DCG Charles Orbih) a ranar Juma’a, 12 ga Satumba, 2025, ya mika ragamar shugabancin hedkwatar Hukumar Kwastam ta Najeriya na Yanki ‘A’ ga ACG Mohammed Babandede, inda ya yi kira ga jami’ai da su ci gaba da nuna haɗin kai, ƙwarewa da kuma gaskiya a ayyukansu. A cikin…
Tinubu Ya Soke Harajin Kashi 5% Kan Sadarwar da Intanet
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ta soke harajin kashi 5% da ake karɓa a kan ayyukan sadarwa, wanda ya haɗa da kiran murya da amfani da bayanan intanet. Hukumar Wayar Tarho ta Ƙasa (NCC) ta bayyana hakan ne ta bakin Babban Kwamishinan Hukumar, Dr. Aminu Maida, inda ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne…
Dauke Wutan Lantarki Zai Zama Tarihi Nan ba da Dadewa ba – Minista
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Najeriya na kan turbar dorewar samar da wutar lantarki. Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana haka a Abuja yayin kaddamar da gine-gine guda biyu da ke dauke da dakunan koyarwa biyar da kuma masaukin ɗalibai mai ɗakuna 104 a Cibiyar Horar da Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Najeriya (NAPTIN)….
Tinubu Zuwa ga FEC: Ku Tabbatar da Saukan Farashin Kayan Abinci
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC) umarnin gaggawa domin ɗaukar matakai da za su taimaka wajen rage farashin abinci a fadin Najeriya. Ministan Jiha na Ma’aikatar Noma da Tsaron Abinci, Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin wani taron horaswa na…
Babban Layin Wutar Lantarki na Ƙasa ya Sake Faduwa
Grid ɗin wutar lantarki na ƙasa ya samu rugujewa a ranar Laraba, lamarin da ya jefa ƙasar cikin duhu baki ɗaya. Bisa bayanan da Independent System Operator (ISO) ta fitar, an tabbatar da cewa yawan samar da wutar lantarki ya faɗi daga 2,917.83 megawatts (MW) zuwa kawai 1.5MW tsakanin ƙarfe 11:00 na safe zuwa 12:00…
NUPENG Ta Janye Yajin Aiki Bayan DSS ta Sasanta su da Kamfanin Dangote
Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas na Najeriya (NUPENG) ta janye yajin aikin da ta fara a faɗin ƙasa bayan cimma matsaya da kamfanin Dangote Group. Yajin aikin, wanda ya fara ne a ranar Litinin, ya samo asali ne daga ƙin amincewar kamfanin da ma’aikatansa su shiga cikin ƙungiyar. An kawo ƙarshen yajin aikin ne…
Majalisar Wakilai Ta Ba Ministan Sufurin Sa’o’i 48 Ya Bayyana Gabanta
Kwamitin Majalisar Wakilai na harkokin sufurin ƙasa ya ba Ministan Sufuri, Sa’idu Ahmed Alkali, wa’adin sa’o’i 48 ya bayyana a gaban kwamitin kan hatsarin da ya rutsa da jirgin ƙasa daga Kaduna mai ɗauke da fasinjoji 618. Kwamitin ya bayar da wannan umarni ne a ranar Talata bayan Ministan ya kasa halartar zaman binciken da…

