Trends

Jirgin Ƙasa: Abuja–Kaduna Zai Fara Aiki Nan da Mako – NRC

Hukumar Jiragen Ƙasa ta Ƙasa (NRC) ta sanar a ranar Asabar cewa sabis na jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna zai koma aiki nan da mako mai zuwa.

Wannan ya biyo bayan kammala gyare-gyare da binciken tsaro a ɓangaren layin da aka lalace.

A tunawa, an dakatar da aikin jirgin ne bayan hatsarin da ya faru a ranar 26 ga Agusta, 2025, lokacin da wani jirgi ya yi hatsari.

Babban jami’in hulɗa da jama’a na NRC, Callistus Unyimadu, wanda ya tabbatar da shirin komawa aiki, bai fayyace takamaiman ranar da aikin zai fara ba.

Ya bayyana cewa hukumar ta “yi aiki tukuru domin tabbatar da cewa kayayyakin more rayuwa da jiragen an dawo da su cikin matakan tsaro na zamani kamar yadda ake yi a duniya.”

Ya ƙara da cewa:
“Don nuna kulawar mu ga fasinjoji, NRC ta maido da kuɗin tikiti ga fasinjoji 512 daga cikin 583 da suka kasance cikin jirgin da hatsarin ya rutsa da shi.

“Ana ci gaba da kokarin tuntubar sauran fasinjojin domin tabbatar da cewa kowa ya samu hakkinsa.”

Hukumar ta gode wa fasinjoji bisa haƙuri da fahimtar da suka nuna, tare da tabbatar da cewa tsaro, kwanciyar hankali da jin daɗin su na ci gaba da kasancewa babban abin da ake baiwa muhimmanci.

Haka kuma, NRC ta yaba da goyon bayan Ma’aikatar Sufurin Ƙasa ta Tarayya, hukumomin tsaro, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki a wannan lokaci na farfaɗowa.

“Za mu sanar da cikakken bayani kan ranar da za a fara aiki da jadawalin tafiya a kwanaki masu zuwa,” in ji hukumar.