Dauke Wutan Lantarki Zai Zama Tarihi Nan ba da Dadewa ba – Minista

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Najeriya na kan turbar dorewar samar da wutar lantarki.

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana haka a Abuja yayin kaddamar da gine-gine guda biyu da ke dauke da dakunan koyarwa biyar da kuma masaukin ɗalibai mai ɗakuna 104 a Cibiyar Horar da Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Najeriya (NAPTIN).

Adelabu ya bayyana cewa wannan ci gaba babban mataki ne ga cibiyar da kuma fannin samar da wutar lantarki, yana mai jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta nuna sahihancin kudirinta ta hanyar “aiwatar da ayyuka bisa hangen nesa.”

Ya ce kokarin gwamnati ya fara haifar da sakamako, inda kasar ta samu mafi girman adadin samar da wuta da kuma watsawa a tarihin ta.

“Ba da jimawa ba, za mu shaida kasar da za ta rika samun wutar lantarki ba kakkautawa 24/7. Wannan abu ne mai yiwuwa, kuma mun riga mun fara ganin alamunsa,” in ji shi.

Ministan ya bayyana cewa gwamnati na haskaka jami’o’i, asibitocin koyarwa, cibiyoyin lafiya, makarantun gwamnati da al’umma, yana mai jaddada cewa wutar lantarki ita ce ginshikin ci gaban sauran bangarorin tattalin arziki, ciki har da ilimi, lafiya da jiragen sama.

“Muna da duk abin da ake bukata domin fara kera na’urorin auna wuta, igiyoyi, injinan canza wuta da batir. Muna da basira. Muna da mutane. Dole mu dogara da kanmu kuma mu dore. Kuma muna kusa da cimma wannan burin,” in ji shi.

Adelabu ya ce sabbin gine-ginen sun nuna aniyar gwamnati na gina ma’aikata masu kwarewa wajen fuskantar kalubale a fagen makamashi da ke kara sauyawa.

Ya kara da cewa cibiyoyin horarwa da masaukin za su bai wa matasa ’yan Najeriya kayan zamani da ilimi da za su taimaka wajen kirkire-kirkire da samar da ayyukan yi.

Daraktan Janar na NAPTIN, Ahmed Nagode, ya bayyana cewa wadannan ayyuka suna zama tubali na makoma mai haske ga fannin samar da wutar lantarki.

Ya ce cibiyar na shirin hada kai da kungiyoyi domin aiwatar da shirin Next Generation Rescue Programme don horar da matasan shugabannin Najeriya tare da ba su dama.

Nagode ya gode wa Tarayyar Turai (EU) da Gwamnatin Faransa, wadanda ta hannun Hukumar AFD suka samar da kudade da taimakon fasaha wajen gina cibiyoyin.

Jakadan EU a Najeriya, Gautier Mignot, ya ce EU ta bayar da tallafin Yuro miliyan 8 domin wannan shiri a matsayin goyon baya ga sauye-sauyen fannin wutar lantarki a Najeriya. Ya ce EU ta taimaka wajen samar da kwasa-kwasai 95 a NAPTIN, ciki har da 65 na fasaha da 30 marasa fasaha, tare da saka sama da Yuro miliyan 200 a fannin wutar lantarki a Najeriya tun daga 2008.

Mignot ya kuma bayyana cewa sabon kunshin zuba jari na makamashi mai sabuntawa na EU a Najeriya mai darajar Yuro miliyan 100 zai kara megawatt 400 na makamashi kafin 2027.