Category: Business
Business
Gwamnatin Tarayya Ta Roki NUPENG da NLC Su Soke Yajin Aiki da Suke Son Gudanarwa
Gwamnatin Tarayya ta roki kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (NUPENG) da kuma kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da su sake duba shirin shiga yajin aikin kasa baki daya da suka sanar a kan Kamfanin Dangote bisa zargin hana kafa kungiyoyin kwadago, tana mai jaddada cewa tattaunawa ita ce mafita mafi inganci wajen warware…
Hukumar Shige da Fice Ta Ƙara Kuɗin Fasfo Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta amince da ƙarin kuɗin biyan fasfo ɗin Najeriya, wanda zai fara aiki daga 1 ga Satumba, 2025. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), A.S. Akinlabi, ya fitar a ranar Alhamis. Akinlabi ya bayyana cewa ƙarin kuɗin ya zama…
Abuja – Kaduna: NRC ta Dakatar da Zirga-Zirgar Jirgin Kasa Bayan Hatsari
Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta dakatar da dukkanin zirga-zirgar jirgin kasa a hanyar Abuja–Kaduna bayan hatsarin da ya faru a ranar Lahadi, inda jirgi ya yi hatsari. Manajan Darakta na NRC, Kayode Opeifa, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka yi a Abuja. Ya bayyana cewa ba za…
Tattalin Arziki: Mulki na Cin Hanci ya Zama Tarihi a Najeriya – Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa masu saka hannun jari na ƙasar Brazil cewa gyare-gyaren tattalin arziƙin da ake aiwatarwa a Najeriya suna samar da ingantattun sakamako, inda ya yi iƙirarin cewa “ba a sake samun cin hanci da rashawa ba” tun bayan da ya hau kujerar shugaban ƙasa. Jaridar Tribune ta rawaito…
Kamfanin BF SUMA Mai Sarrafa Magunguna daga Saiwoyi Ya Dawo Aiki a Kano
Kamfanin BF SUMA wanda ya kasance babban kamfanin sarrafa magunguna da saiwoyi na ƙasar Amurka ya dawo Kano Najeriya bayan dogon loƙaci da aka ɗauka kamfanin ba ya Najeriya. A ranar Laraba ne 20 ga watan Agusta aka yi gagarumin bikin sake ƙaddamar da reshen kamfanin na jihar Kano bayan kamfanin ya yi ƙaura daga…
Tinubu Ya Soke Harajin Kashi 5%na Sadarwa — NCC
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya soke harajin kashi 5% da ake ɗora wa kan ayyukan sadarwa, matakin da aka bayyana zai rage wa ’yan kasa da kamfanoni nauyin kuɗi a tattalin arzikin zamani na dijital. Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), Aminu Maida, ne ya bayyana hakan a lokacin taron manema labarai da aka…
NCC Ta Yi Alkawarin Inganta Sabis da Kare Hakkin Jama’a a Fannin Sadarwa
Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta sake jaddada aniyarta na inganta ingancin sabis, gaskiya da kare hakkin masu amfani da wayar salula a ƙasar. Mataimakin Shugaban Hukumar (EVC), Dakta Aminu Maida, ne ya bayyana haka a wani taron tattaunawa da manema labarai a Abuja, inda ya gabatar da muhimman dabaru da ake amfani da su…
NCAA ta Haramta Amfani da “airplane mode”, ta Umarci Fasinjoji su Kashe Waya
Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta bayyana cewa dukkan wayoyin hannu dole ne a kashe gaba ɗaya yayin tashin jirgi da kuma lokacin sauka. Daraktan Hukumar, Kyaftin Chris Najomo, ne ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki na “National Civil Aviation Security Committee Meeting” da aka gudanar a Abuja…
Najeriya Za ta Fitar da Kaya Zuwa China ba Tare da Biyan Haraji ba – Hongyou
Najeriya na daga cikin ƙasashen Afirka 53 da za su ci gajiyar fitar da kayayyaki zuwa China ba tare da biyan haraji ba, wani ci gaban da hukumomi suka bayyana a matsayin babban ƙarin ƙarfi ga harkokin kasuwanci da haɗin tattalin arziƙi. Wannan sanarwa ta fito ne a yayin bikin al’adu da yawon shakatawa na…
NTA: Tinubu Ya Naɗa Pedro a Matsayin Sabon Shugaban Gidan Talabijin na Kasa
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi babban sauye-sauye na shugabanci a gidan talabijin na ƙasa (NTA), inda ya naɗa Rotimi Richard Pedro, a matsayin sabon Darakta-Janar na gidan talabijin din na gwamnati. “Sauran manyan nade-naden sun haɗa da Karimah Bello daga Jihar Katsina a matsayin Daraktar Tallace-Tallace, Stella Din daga Jihar Filato a matsayin…

