Gwamnatin Tarayya Ta Roki NUPENG da NLC Su Soke Yajin Aiki da Suke Son Gudanarwa

Gwamnatin Tarayya ta roki kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (NUPENG) da kuma kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da su sake duba shirin shiga yajin aikin kasa baki daya da suka sanar a kan Kamfanin Dangote bisa zargin hana kafa kungiyoyin kwadago, tana mai jaddada cewa tattaunawa ita ce mafita mafi inganci wajen warware rikici.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, Shugabar Sashen Bayani da Hulda da Jama’a, Patience Onuobia, ta bayyana cewa Ministan Kwadago da Ayyukan Yi, Muhammad Maigari Dingyadi, ya shiga tsakani kuma ya gayyaci dukkan bangarorin zuwa taron sulhu da aka tsara gudanarwa a ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025.

Dingyadi ya bukaci NUPENG da ta janye matsayinta na rufe bangaren man fetur na kasa, yana gargadin cewa ko da yajin aiki na kwana daya zai iya haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasa da jin dadin ‘yan Najeriya. Haka kuma ya roki NLC da ta janye gargadin yajin aiki na hadin kai da ta baiwa kungiyoyin da ke karkashinta domin goyon bayan NUPENG kan zargin tsare-tsaren cin zarafi ga ma’aikata da ake tuhumar Kamfanin Dangote da su.

Ministan ya ce: “Na gayyaci dukkan bangarorin zuwa taron sulhu gobe, Litinin, 8 ga Satumba, 2025. Tun da na shiga tsakani, ina rokon NUPENG da ta janye kudurinta na rufe bangaren man fetur. Haka kuma ina rokon NLC da ta janye gargadin da ta baiwa kungiyoyinta domin shirin shiga yajin aiki na kasa baki daya don goyon bayan NUPENG.”

Yayin da yake jaddada hadarin da ke tattare da katse samar da man fetur, Dingyadi ya bayyana cewa bangaren man fetur shi ne ginshikin tattalin arzikin kasar. Ya ce yajin aiki a wannan bangare ba wai kawai zai haifar da asarar kudaden shiga da suka kai biliyoyin naira ba, har ma zai jefa ‘yan Najeriya cikin tsananin kunci saboda dogaro da man fetur wajen rayuwar yau da kullum da harkokin tattalin arziki.

Ya ce: “Bangaren man fetur na da matukar muhimmanci ga wannan kasa. Shi ne tushen tattalin arzikin kasa. Idan aka yi yajin aiki a wannan bangare, ko na kwana daya ne, zai janyo illa ga tattalin arzikin kasa. Ba wai kawai zai haifar da babbar asarar kudaden shiga ba, har ma zai jefa ‘yan Najeriya cikin matsananciyar wahala.”

Dingyadi ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnatin tarayya na da cikakken niyyar warware lamarin cikin lumana, tare da nuna kwarin gwiwa cewa tattaunawa da hadin kai za su samar da mafita mai dorewa da za ta kare hakkin ma’aikata, ta mutunta kungiyoyin kwadago, kuma ta tabbatar da kwanciyar hankali a bangaren man fetur.

Ya kammala da cewa: “Saboda haka, ina rokon kungiyoyin da su baiwa zaman lafiya dama. Ina tabbatar musu cewa za a warware wannan matsala cikin lumana har kowa ya gamsu.”