Masana sun sanar cewa Najeriya na daga cikin kasashen da za su shaida cikakkiyar fafarewar wata (lunar eclipse) a ranar Lahadi, 7 ga Satumba, 2025. Wannan al’amari zai faru daga yammacin Lahadi zuwa tsakar dare, kuma zai dauki tsawon mintuna 82.
Yaya Fafarewar Wata Ke Faruwa?
Fafarewar wata na faruwa ne lokacin da duniyar mu ta shiga tsakanin rana da wata, ta yadda kasa ke rufe hasken rana daga kai tsaye zuwa ga wata. A irin wannan yanayi, hasken da ke bayyana daga fuskar wata shi ne wanda yanayin kasa ya karkatar. Wannan shi ne dalilin da yasa fafarewar ke bada haske mai duhu ko ja.
Inda Za a Iya Gani
Cikakkiyar fafarewar za a iya kallonta a Najeriya tun daga lokacin da wata ya fara shiga inuwa har sai ya sake bayyana.
Haka kuma za a iya ganinta a kasashen Togo, Kamaru, Gabon, Equatorial Guinea, Benin, Ghana, Chadi, Nijar, da Sao Tome da Principe.
Wasu sassan duniya irin su Asiya, Ostiraliya da Turai ma za su ga wannan al’amari.
Amma kasashen Spain da Norway za su shaida rabin fafarewa (partial eclipse) kawai.
Shin Lafiya Ne a Kalla?
Masana sun bayyana cewa fafarewar wata ba ta bukatar kariya ta musamman kamar tabarau na musamman da ake amfani da su wajen kallo lokacin fafarewar rana. Wannan saboda hasken fafarewar wata yakan yi rauni fiye da cikakken wata, don haka yana da lafiya a kalla da ido kai tsaye.
Muhimmancin Al’amari
Masana kimiyyar sararin samaniya suna ganin irin wadannan al’amura na nuna yadda duniyoyi ke tafiya cikin tsarin da Allah ya halitta. Suna kuma ba da dama ga mutane su koyi karin bayani kan sararin samaniya da dangantakar rana, kasa da wata.
