Kisan Mutane 100 a Karshen Mako Alamar Najeriya Ta Shiga Hali Tashin Hankali – Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP) a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana kisan da aka yi a jihohin Borno, Edo, Sokoto da Katsina a makon da ya gabata a matsayin abin “firgita”, yana mai cewa hakan hujja ce cewa Najeriya na cikin cikakken hali na gaggawar tsaro.

Obi ya bayyana hakan ne a rubutunsa na ranar Lahadi a shafin X (tsohon Twitter). Rahotanni sun nuna cewa a Darul Jamal, karamar hukumar Bama ta jihar Borno, ‘yan ta’addan Boko Haram sun kashe fararen hula da dakarun soja da dama.

A jihar Katsina kuwa, ‘yan bindiga sun kashe mutane shida tare da yin garkuwa da sama da mutum 130 a cikin kwanaki uku kacal a yankin karamar hukumar Sabuwa.

A Edo, a daren Juma’a, masu garkuwa da mutane sun kashe jami’an hukumar tsaro ta NSCDC guda takwas tare da yin garkuwa da wani ɗan kasar China a Okpella, karamar hukumar Etsako ta Gabas.

Da yake mayar da martani, Obi ya ce wadannan hare-haren ba al’amura ne da za a dauka da wasa ba, domin sun nuna a sarari cewa Najeriya na cikin “cikakken yanayin gaggawar tsaro.” Ya kara da cewa kashe sama da ‘yan Najeriya 100 a cikin mako guda ya kusan kai Najeriya irin halin da kasashen da suke cikin yakin basasa ke fuskanta.

Obi ya rubuta cewa: “Najeriya na zubar da jini, dole ne a ayyana yakin gaggawa kan matsalar tsaro yanzu. Kashe jami’an NSCDC guda takwas, garkuwa da dan kasar Sin a Edo, sace fasinjoji a kan hanyar Benin–Iyere–Oluku, da kuma kisan sojoji biyar tare da fararen hula 58 a Borno, ba karamin bala’i bane. Wannan hujja ce ta yadda lamarin ya tsananta.”

Ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, yana mai cewa: “Ina mika gdeepest condolences ga iyalan jaruman da suka fadi. Jarumtarsu tana tunatar damu cewa har yanzu akwai mata da maza masu jajircewa wajen kare rayukanmu. Dole ne gwamnati ta kama wadanda suka aikata wannan mummunan aiki ta kuma tabbatar da an hukunta su. Ba za a taba mantawa da hadayarsu ba.”

Obi ya bukaci gwamnati ta dakatar da duk wata “sha’awa mai jan hankali” ta mai da hankali wajen dakile wannan annobar tsaro. Ya ce: “Lokacin da aka kashe sama da mutane 100 a cikin karshen mako guda, kididdigar mutanen da ake rasa ta yi kama da ta kasashen da suke cikin yaki. Wannan ba lokacin wasa bane. Ya kamata a ayyana yakin kasa na gaggawa kan matsalar tsaro, a hada dukkan albarkatu, hukumomi, jihohi, a kuma dakatar da duk wani abu na jan hankali.”

Ya kuma bukaci a dakatar da yawon kasashen waje na jami’an gwamnati har sai an shawo kan lamarin. “Jagoranci na gaskiya dole ne a gani a gida, shugaban kasa da gwamnati suna tsaye suna jagorantar wannan yaki da rashin tsaro. Tafiya kasashen waje a lokacin da kasa ke zubar da jini don neman masu zuba jari, kamar wauta ce. Babu wani mai saka jari da zai zo kasar da ke cikin yanayin yaki.”

Obi ya yi gargadi cewa babu wata kasa da za ta ci gaba yayin da ‘yan kasarta ke rayuwa cikin fargaba, yana mai cewa tarihin kasashen Somalia da Libya ya isa darasi mai tsanani.

Ya kammala da cewa: “Dole ne mu dauki mataki yanzu da gaggawa da jarumta domin kare kasar mu daga fadawa cikin rudani gaba daya, mu kuma gina Najeriya cikin kasa mai aminci da kwanciyar hankali ga kowa. Sabuwar Najeriya zai yiwu”