Kamfanin BF SUMA wanda ya kasance babban kamfanin sarrafa magunguna da saiwoyi na ƙasar Amurka ya dawo Kano Najeriya bayan dogon loƙaci da aka ɗauka kamfanin ba ya Najeriya.
A ranar Laraba ne 20 ga watan Agusta aka yi gagarumin bikin sake ƙaddamar da reshen kamfanin na jihar Kano bayan kamfanin ya yi ƙaura daga Najeriya bayan fuskantar matsin tattalin arziƙi da kamfanin ya yi a ƙasar.
Taron wanda aka gudanar a sabon babban ofishin kamfanin da ke Kano ya samu halartar masana harkar lafiya da dama tare da ɗimbin al’umma wanda suka yaba da irin ƙoƙarin da aka yi wajen ganin cewa an dawo da wannan kamfani na Najeriya tun bayan ficewarsu daga ƙasar tsawon shekaru.
Kamfanin wanda ya yi fice wajen bincike tare da bayar da magungunan na gargajiya wanda ke da hedikwata a Amurka a yanzu ya dawo bakin aiki a Kano bayan faɗi-tashi da aka yi har aka yi nasarar dawo da shi Najeriya da wasu daga cikin waɗanda suke karɓar magani a kamfanin suka yi.
Dakta Ali Mujahid mai shekara 52 ya nuna farin cikinsa kan yadda suka yi nasara har aka dawo da kamfanin a nan garin Kano. Ya ce tsaiko da aka samu na shekarun baya da ba kamfanin ya sa marasa lafiya da dama sun shiga wani hali, musamman manya da suke karɓar magungunan bunƙasa garkuwar jiki.

A cewar Dakta Ali, “ya ce yana da mara lafiya mai ɗauke da cutar sikila wanda ya gwada magunguna da dama amma maganin BF SUMA shi ne maganin da ya fi jin daɗin amfani da shi a koyaushe”.
Ya ƙara da cewa yakan je asibiti sukan ba shi magani amma da ke sinadaran kemical ne suka fi yawa kuma, sau tari sukan kwantar da cuta ne ba tare da samun sauƙi ba.
Dakta Faiz Sarki, masani kuma mai horaswa kan cututtukan da dama a kamfanin ya ƙara da cewa mutane da dama sun damu bayan ficewar kamfanin daga Najeriya, amma Alhamdulillah yanzu an yi nasarar dawo da kamfanin bayan dogon nazari da aka sha tsakanin kamfanin da kuma masu buƙata.
Amina Kabir Sulaiman Zogarawa, na ɗaya daga wacce ta yi farin ciki da dawowar kamfanin wacce ta ce tun bayan ficewar kamfanin ta shiga cikin damuwa sakamakon rashin samun irin maganin da ta saba amfani da shi.
Marasa lafiya sun bayyana farin cikinsu bisa kokari da aka yi na dawo da kamfanin maganin gargajiya na zamani na BF SUMA a Kano, Najeriya.
A lokacin da kamfanin ya tattare ya bar Najeriya, sai Kenya muke turawa a kawo mana maganin saboda babu yadda za mu yi.
A yayin taron an yi kira da al’umma da su rika lura da lafiyarsu tare da shan magungunan na asali waɗanda ba sa janyo illa ga garkuwar jiki.




Alhmdllh mungodewa Allah da dawowar wannan kamfanin Nigeria