Gwamnatin Tarayya ta amince da ƙarin kuɗin biyan fasfo ɗin Najeriya, wanda zai fara aiki daga 1 ga Satumba, 2025.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), A.S. Akinlabi, ya fitar a ranar Alhamis.
Akinlabi ya bayyana cewa ƙarin kuɗin ya zama dole domin tabbatar da inganci da amincin sabon fasfo ɗin Najeriya da za a fara amfani da shi daga watan Satumba.
“Wannan sauyin ya shafi kuɗin neman fasfo kawai da ake yi a Najeriya. Sabon tsarin ya kayyade cewa fasfo mai shafuka 32 da ke da ingancin shekaru 5 zai kasance ₦100,000, yayin da fasfo mai shafuka 64 da ke da ingancin shekaru 10 zai kasance ₦200,000,” in ji shi.
Sai dai ya ƙara da cewa, kuɗin neman fasfo da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ke biya ba su canza ba. Za a ci gaba da cajin $150 ga fasfo mai shafuka 32 da ke da ingancin shekaru 5, da kuma $230 ga fasfo mai shafuka 64 da ke da ingancin shekaru 10.
Hukumar Shige da Fice ta nanata aniyar ta na tabbatar da ingantaccen hidima tare da kula da samun damar yin fasfo ga dukkan ‘yan Najeriya cikin sauƙi da adalci.
