An kama wani jami’in ‘yan sanda a ƙaramar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi, bisa zargin harbe wani soja har lahira a garin Futuk.
Mataimakin Daraktan watsa labarai na rundunar sojoji, 33 Artillery Brigade, Atang Hallet Solomon, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai. Ya ce an kama ɗan sandan da ake zargi ya harbi sojan, kuma yanzu haka ana gudanar da bincike tare tsakanin sojoji da ‘yan sanda domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma hana ƙara rikici.
Rahotanni daga mafarauta da ‘yan sa-kai a Futuk sun ce lamarin ya samo asali ne daga takaddama tsakanin jami’an tsaro kan wata motar ɗaukar kaya mallakar kamfanin hakar ma’adinai na ƙasar Sin.
Sun bayyana cewa an tare motar, wadda ke ɗauke da ma’adinai daga wurin hakar Yalo, da yamma bayan sallar magariba a ranar Litinin.
Shaidu sun ce sojojin rundunar 33 Artillery Brigade sun umarci direban motar da ke ɗauke da lambar rijista Gombe 676 BLG da ya tsaya a shingen bincike, amma ya ƙi. Wannan ya sa sojojin suka bi shi har suka tare motar kusa da gada.
A cewar wani shaidar idanu:
“Sai rikici ya barke tsakanin jami’in soja mai jagorantar tawagar da ɗan sandan MOPOL da ke raka motar. A lokacin wannan arangama ne ɗan sandan ya ɗaga bindigarsa ya harbi sojan a bayansa.”
Lamarin ya jefa mazauna yankin cikin fargaba, inda ‘yan kasuwa suka rufe shagunansu cikin gaggawa, yayin da direban motar ya tsere cikin hayaniya.
Hukumar ƙaramar hukumar Alkaleri ta yaba wa sojojin da suka nuna haƙuri, inda maimakon su ɗauki fansa, suka cafke direban motar tare da ɗan sandan da aka zarga bayan sun kwace masa bindiga, sannan suka mika su zuwa Bauchi domin ci gaba da bincike.
An garzaya da sojan da aka harba zuwa asibiti a Gombe, amma daga bisani ya rasu. An ajiye gawarsa a dakin ajiye gawa, yayin da ake shirin jana’izarsa bisa tsarin soja.
Rahotanni sun nuna cewa ɗan sandan MOPOL yana nan a tsare, yayin da aka kwace motar ma’adinai.
Ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ya ci tura, domin Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Ahmed Wakil, bai ɗaga kira ko ya amsa sakonni ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.
Mafarauta a yankin sun bayyana cewa motar na ɗauke da ma’adinai da ake zargin an hako su ba bisa ka’ida ba daga ƙauyen Yalo, kuma ɗan sandan da aka kama na iya kasancewa cikin wani aikin rakiyar da bai dace ba.
Sun ce ƙin tsayawar motar a shinge, harbin soja daga hannun jami’in ‘yan sanda, da kuma guduwar direban, duk sun ƙara tabbatar da cewa sai bincike mai zurfi zai iya fayyace gaskiyar lamarin.
Hukumar ƙaramar hukumar ta kuma nuna damuwa cewa shiga hannun jami’an tsaro cikin harkokin hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba yana ƙara yawaita, tare da kira ga hukumomin ƙoli da su kawo ƙarshen wannan matsala.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi ya gana da kwamandan rundunar 33 Artillery Brigade, Brig.-Janar U.J. Simon, domin rage tashin hankali da kuma tabbatar da cewa an gudanar da shari’ar bisa ka’ida.
