Trends

Zaɓen Fidda Gwani: Goje Ya Sha Kaye Yayin da DCP Mohammed Ya Lashe Tikiti

Sanata Muhammad Danjuma Goje ya rasa tikitin jam’iyyar APC na takarar Sanatan Gombe Ta Tsakiya, bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani da aka gudanar ranar Litinin.

A zaben kai tsaye da aka gudanar a kananan hukumomin Akko da Yamaltu/Deba, wadanda su ne suka kunshi mazabar Gombe Ta Tsakiya, tsohon jami’in dan sanda, DCP Mohammed Ahmed mai ritaya, ya lashe tikitin jam’iyyar.

Jami’in da ke sanar da sakamakon zaben, Dr Habu Dahiru, ya bayyana cewa DCP Ahmed ya samu kuri’u 42,785, yayin da Muhammad Danjuma Goje ya samu kuri’u 10,425 kacal.

Tun kafin gudanar da zaben, jam’iyyar APC ta zabi DCP Mohammed Ahmed a matsayin dan takarar hadin kai (consensus candidate) na kujerar Sanatan Gombe Ta Tsakiya.

Muhammad Danjuma Goje ya wakilci yankin a Majalisar Dattawa tun daga shekarar 2011 bayan kammala wa’adinsa biyu a matsayin gwamnan jihar Gombe.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan sakamako na nuna babban sauyi a siyasar Gombe Ta Tsakiya.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaben fidda gwani, DCP Mohammed Ahmed ya ce an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.

Ya ce yanayin zaben ya nuna yadda jama’a ke nuna goyon baya ga sauyi a yankin Gombe Ta Tsakiya.

A cewarsa, mambobin jam’iyyar da mazauna yankin sun nuna farin ciki da yiwuwar samun wakilci mafi karfi a Majalisar Dokoki ta Kasa.

Ya ce, “Kowa na iya ganin farin cikin jama’a. Da yawa sun yi imanin cewa lokaci ya yi da Yamaltu-Deba za ta samu murya mafi karfi a matakin kasa.”

Dan takarar APC din ya kara da cewa burinsa ba wai hana wani tsayawa takara ba ne, “amma yana fitowa ne daga bukatar jama’a na ganin sabon alkibla.”

Lokacin da aka tuntubi daya daga cikin mataimakan Muhammad Danjuma Goje domin jin ta bakinsa, ya ki yin tsokaci, yana mai cewa sai ya samu izini daga ubangidansa kafin yin magana da manema labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *