Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa kan Rancen $516m
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya rubuta wa majalisar dattawa wasika yana neman amincewarta domin karɓo sabon rance na dala miliyan 516,333,070. A cikin wasikar da aka aike wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, wadda aka karanta a zaman majalisar na ranar Alhamis, an bayyana cewa za a karɓo rancen ne daga Deutsche Bank. Wasikar ta…
