Bola Tinubu ya sallami Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsara Tattalin Arziki, Wale Edun, tare da Ministan Gidaje da Raya Birane, Umar Dangiwa.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ne ya sanar da hakan cikin wata takarda.
An umurci Edun da ya miƙa ragamar aiki ga Taiwo Oyedele, wanda yanzu zai zama Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsara Tattalin Arziki. Kafin haka, Oyedele ya riƙe mukamin Karamin Ministan Kuɗi.
Haka kuma, an bayyana Muttaqha Rabe Darma a matsayin wanda aka naɗa domin zama Ministan Gidaje da Raya Birane, yayin da aka umurci Dangiwa da ya miƙa aiki ga Karamin Ministan da ke ma’aikatar.
Takardar ta bayyana cewa dukkanin hanyoyin miƙa da karɓar aiki dole ne a kammala su kafin ƙarshen aiki na ranar Alhamis, 23 ga Afrilu, 2026.
Da yake bayani kan matakin, Akume ya ce sauye-sauyen na da nufin ƙarfafa haɗin kai da inganta aiki a gwamnati, tare da samar da sakamako mai tasiri ga tattalin arzikin ƙasa karkashin shirin “Renewed Hope Agenda”.
Ya ƙara da cewa shugaban ƙasa ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulkin Constitution of the Federal Republic of Nigeria ya ba shi a sashe na 147 da 148 wajen yin wannan sauyi.
Tinubu ya gode wa ministocin da aka sallama bisa gudunmawar da suka bayar ga ƙasa, tare da yi musu fatan alheri a nan gaba. Haka kuma ya tabbatar wa sauran mambobin majalisar ministoci cewa za a ci gaba da sabunta tsarin gwamnati domin inganta aiki.


