CBN, NCC Sun Kulla Yarjejeniya Don Yaƙi da Damfarar SIM

Central Bank of Nigeria da Nigerian Communications Commission sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna domin yaƙi da damfarar da ta shafi layukan waya (SIM) da kuma ƙarfafa kariyar masu amfani a tattalin arzikin dijital na Najeriya.

An sanya hannu kan yarjejeniyar a hedikwatar CBN da ke Abuja, inda aka ce za ta inganta haɗin gwiwa tsakanin bangaren kuɗi da na sadarwa, musamman wajen dakile damfarar lantarki da ke da alaƙa da lambobin waya da kuma ƙarfafa ingancin tsarin biyan kuɗi.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin “mataki mai amfani ga ƙasa,” yana mai cewa yawaitar amfani da hanyoyin dijital na buƙatar ƙarin haɗin kai tsakanin masu tsara dokoki.

Ya ce yarjejeniyar za ta ƙarfafa haɗin kai a fannin amincewa da tsare-tsare, ƙa’idojin fasaha da gwaje-gwajen sabbin abubuwa, tare da inganta martani ga karuwar damfarar intanet. Ya ƙara da cewa magance waɗannan barazana na buƙatar haɗin gwiwa, musayar bayanai, ingantattun hanyoyin daukar mataki, da kuma wayar da kan jama’a.

Wani muhimmin ɓangare na yarjejeniyar shi ne ƙaddamar da dandalin “Telecom Identity Risk Management Portal,” wanda zai ba da damar tabbatar da matsayin lambobin waya a lokaci guda tsakanin bankuna da kamfanonin fintech, domin gano damfara da ke da alaƙa da layukan da aka sake amfani da su, aka canza, ko aka sanya su a jerin baƙaƙe.

Shugaban zartarwa na NCC, Aminu Maida, ya ce wannan yarjejeniya babban ci gaba ne, yana mai jaddada cewa haɗin gwiwa tsakanin cibiyoyin biyu ba zaɓi ba ne, wajibi ne. Ya ce shirin zai ba cibiyoyin kuɗi damar fahimtar lambobin waya da ake amfani da su wajen ma’amaloli.

Hadin gwiwar ya ginu ne kan wasu matakai na baya, ciki har da warware rikicin farashin USSD, ƙaddamar da kuɗin Naira 6.98 ga kowane amfani, da kuma shirin dawo da kuɗi cikin daƙiƙa 30 ga ma’amalolin da suka gaza.

Kwamitoci guda biyu ne za su kula da aiwatar da yarjejeniyar: ɗaya kan tsarin biyan kuɗi da kariyar masu amfani, ɗaya kuma kan kula da haɗarin sadarwa. Hukumomin sun ce yarjejeniyar za ta ƙara faɗaɗa hada-hadar kuɗi, rage damfara, da kuma ƙarfafa amincewa a tattalin arzikin dijital na ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *