Category: Business
Business
Harkokin Zuwa Jarin Waje na NGX Sun Fāɗi da Kashi 75%
Shigar masu zuba jari na ƙasashen waje a kasuwar hannayen jari ta Nigerian Exchange Limited (NGX) ta yi mummunar fāɗuwa a watan Janairun 2026, inda ta ragu da kashi 75.08 cikin ɗari cikin wata guda kacal. Bayanai daga rahoton Domestic and Foreign Portfolio Investment sun nuna cewa ma’amalolin ‘yan waje sun sauka daga Naira tiriliyan…
Najeriya Ta Samu Hada – Hada Kuɗin Noma Naira Tiriliyan 101.46 a 2025
Sashen noma na Najeriya ya kai jimillar juyin kuɗi na Naira tiriliyan 101.46 a shekarar 2025, daga Naira tiriliyan 96.46 da aka samu a shekarar da ta gabata. Wannan ci gaban, wanda ya samu sakamakon ƙaruwa a zuba jari, ya sa adadin haɓakar sashen a zahiri ya tashi daga kashi 1.69 cikin ɗari zuwa kashi…
FG, AFC Sun Kulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 1.3 Domin Gina Matatar Alumina
Gwamnatin Tarayya tare da Africa Finance Corporation (AFC) sun rattaba hannu kan yarjejeniyar dala biliyan 1.3 domin sauya fasalin harkar ma’adinai a Najeriya. An kulla yarjejeniyar ne ta hannun Solid Minerals Development Fund (SMDF), inda ta mayar da hankali kan muhimman ginshiƙai uku: gina babbar matatar alumina, gudanar da taswirar kimiyyar ƙasa a faɗin ƙasar,…
Aerotropolis: Gwamnati Za Ta Sauya Tsarin Filayen Jiragen Sama
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na zuba jari a bangaren sufurin jiragen sama, inda take shirin kafa tsarin aerotropolis — wato hada filayen jiragen sama da biranen kasuwanci, cibiyoyin sufuri da masana’antu — a manyan biranen kasar nan. Ana sa ran kaddamar da shirin a taron Aircraft Acquisition and Investment Summit mai…
Zuba Jari na Waje a Masana’antu Ya Fadi da Kashi 54% – NBS
National Bureau of Statistics suka nuna, zuba jari na waje a bangaren masana’antu na Najeriya ya ragu da kashi 54.11 cikin 100 a cikin watanni tara na farko na 2025, duk da karuwar jimillar shigar jari a kasa baki daya. Bangaren masana’antu ya samu dala miliyan 463.52 kawai, daga dala biliyan 1.01 a lokacin daidai…
Kasuwar Jari Ta Kai 33% na GDP – SEC
Hukumar Kula da Kasuwar Hada-hadar Jari ta Najeriya (SEC) ta bayyana cewa gudunmawar kasuwar jari ga Jimillar Arzikin Cikin Gida (GDP) ta kai kashi 33%, yayin da jimillar darajar kasuwa ta karu zuwa Naira tiriliyan 123.93, daga Naira tiriliyan 55 a watan Afrilun 2024 – karin kaso 125%. Daraktan Janar na Securities and Exchange Commission,…
Matatar Dangote Za Ta Fitar da Hannayen Jari Cikin Watanni 5
Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya sanar da cewa ‘yan Najeriya za su iya sayen hannayen jari a Dangote Refinery cikin watanni hudu zuwa biyar masu zuwa, yayin da kamfanin ke shirin shiga kasuwar hada-hadar jari (listing). Dangote ya bayyana hakan ne lokacin da Shugaban Rukunin Kamfanin Nigerian National Petroleum Company (NNPC), Bayo Ojulari, tare…
Gwamnatin Tarayya ta Ware Kashi 5% na GDP Don Bunkasar Masana’antu.
Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin ware kashi 5 cikin 100 na Jimillar Arzikin Cikin Gida (GDP) na Najeriya a kowace shekara domin tallafa wa harkokin bunkasa masana’antu, karkashin sabon Tsarin Ci gaban Masana’antu na Najeriya (Nigeria Industrial Plan) da aka kaddamar. An bayyana tsarin a Abuja ta hannun Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, inda…
Tinubu Ya Amince da Biyan GenCos Naira Tiriliyan 2.8
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da biyan kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos) Naira tiriliyan 2.8 a matsayin bashin tallafin wutar lantarki da Gwamnatin Tarayya ta tara tun daga shekarar 2010. Matakin ya biyo bayan watanni na tattaunawa da kuma cikakken bincike (audit) na hadin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Kamfanin NBET da…
IPMAN Na Neman Dala Biliyan 10 Domin Gina Matatar Mai
Kungiyar ‘Yan Kasuwar Mai Masu Zaman Kansu ta Najeriya, Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN), na shirin neman rancen kudi domin gina matatar mai ta dala biliyan 10. Matakin ya biyo bayan sauye-sauyen farashi da ake samu daga manyan masu samar da mai a kasuwa, ciki har da Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals (DPRP)….

