Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da biyan kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos) Naira tiriliyan 2.8 a matsayin bashin tallafin wutar lantarki da Gwamnatin Tarayya ta tara tun daga shekarar 2010.
Matakin ya biyo bayan watanni na tattaunawa da kuma cikakken bincike (audit) na hadin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Kamfanin NBET da kuma GenCos. Shugaban ya ki amincewa da bukatar kamfanonin ta Naira tiriliyan 6, yana mai jaddada cewa ba zai biya abin da ya wuce adadin da bincike ya tabbatar ba.
Wata majiya daga Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa, “GenCos sun zo nan watan Agustan bara… sun ce bashin da aka tara tun 2010 ya kai tiriliyan 6. Amma Shugaban ya ce musu, ‘Wannan ikirarin ku ne… ba zan biya tiriliyan 6 don kawai kun fada ba. Za mu yi bincike.’”
A watan Janairu, gwamnati ta tara Naira biliyan 501 ta hanyar fitar da takardar bashi (bond) karkashin shirin rage bashin bangaren wutar lantarki na Shugaban Kasa, inda aka raba kudin a matsayin kyakkyawar niyya yayin da binciken ke gudana. Yanzu da aka kammala binciken, an tabbatar da cewa bashin da ya dace a biya ya tsaya a kan Naira tiriliyan 2.8.
Sai dai Shugaban ya daura sharudda kan yadda za a fitar da kudaden.
Ya umurci cewa wani kaso mai tsoka daga cikin kudin dole ne a yi amfani da shi wajen biyan bashin da GenCos ke bin kamfanonin samar da iskar gas, wanda aka ce shi ne daya daga cikin manyan dalilan yawaitar rushewar layin wutar lantarki a kasa. Wata majiya ta ce, “Gwamnati za ta kayyade adadin da za su biya… domin kada su sake dawowa su ce har yanzu ana bin su bashin gas.”
Ana sa ran za a sake biyan karin Naira biliyan 600 zuwa 800 tsakanin watan Mayu da Yuli, wanda hakan zai kai jimillar kudin da aka biya zuwa kusan rabin adadin da aka amince da shi kafin tsakiyar shekara, yayin da za a raba sauran kudin cikin watanni 12 zuwa 24 masu zuwa.
Binciken da Fadar Shugaban Kasa ta gudanar ya kuma gano cewa akwai karancin saka jari daga bangaren masu gudanar da kamfanonin, inda aka lura cewa GenCos da DisCos na karbar kudaden shiga amma ba sa mayar da isasshen jari wajen inganta kayayyakin aiki da cibiyoyi. Saboda haka, Shugaba Tinubu ya danganta wani bangare na Naira tiriliyan 2.8 da wajabcin sabunta kayayyakin aiki, tare da bukatar a gabatar da hujjojin cika sharuddan kafin a fitar da kudin.
Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta nuna adawa da biyan manyan kudade ga kamfanonin, tana mai bayyana tsarin sayar da kamfanonin gwamnati ga masu zaman kansu a matsayin “babbar yaudara.” Kungiyar ta yi gargadin cewa bai dace a saka wa kamfanonin da suka sayi kadarori kan Naira biliyan 400 lada ba, alhali har yanzu karfin samar da wutar lantarki na kasar na yawo tsakanin megawatt 2,000 zuwa 5,000 ba tare da gagarumin ci gaba ba.
