Gwamnatin Tarayya tare da Africa Finance Corporation (AFC) sun rattaba hannu kan yarjejeniyar dala biliyan 1.3 domin sauya fasalin harkar ma’adinai a Najeriya.
An kulla yarjejeniyar ne ta hannun Solid Minerals Development Fund (SMDF), inda ta mayar da hankali kan muhimman ginshiƙai uku: gina babbar matatar alumina, gudanar da taswirar kimiyyar ƙasa a faɗin ƙasar, da kuma ƙirƙirar wani asusun zuba jari na musamman.
Babban abin da yarjejeniyar ta ƙunsa shi ne gina matatar alumina ta dala biliyan 1.3 wadda za ta rika sarrafa ton miliyan ɗaya na dutsen bauxite a duk shekara.
Za a yi amfani da sabuwar fasahar “Bayer-process” a matatar, tare da samar da wutar lantarki da tururi ta hanyar tashar gas da za a girka a wurin, domin biyan bukatun ayyukanta.
Ministan Ma’adinai, Dele Alake, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin “babbar alama ta ci gaba” yayin bikin sanya hannu a Abuja.
Alake ya jaddada cewa aikin zai ƙara gudunmawar ɓangaren ma’adinai ga Babban Jimillar Kuɗaɗen Shiga na Ƙasa (GDP), tare da samar da dubban guraben ayyukan yi ta hanyar ƙara darajar albarkatun ƙasa a cikin gida.
Hasashen tattalin arziƙi na matatar ya nuna cewa, cikin shekaru 20 da ake sa ran za ta yi aiki, za ta rika ƙara kusan dala biliyan 1.2 a duk shekara ga GDP, tare da samar da kimanin dala biliyan 8 na kuɗaɗen musayar waje, wanda zai taimaka wajen daidaita tattalin arziƙin ƙasa.
Baya ga gina ababen more rayuwa, haɗin gwiwar ya kuma magance ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke hana masu zuba jari shigowa, wato rashin ingantattun bayanai.
Yarjejeniyar ta haɗa da cikakken shirin taswirar kimiyyar ƙasa domin samar da sahihan manyan bayanai (big data) game da dumbin ma’adinan da Najeriya ke da su, da nufin rage haɗarin zuba jari ga masu bincike da kamfanonin ƙasa da ƙasa.
Babbar Sakatariyar SMDF, Hajia Fatima Shinkafi, ta ce wannan shi ne mafi girman aiki a tarihin asusun. Ta bayyana cewa, “Muna alfahari da sauƙaƙa wannan muhimmin ci gaba. Wannan aikin na kashe dala biliyan 1.3 ya nuna cewa SMDF ta kai matakin balaga.”
Domin kauce wa tsaiko daga hukumomi, Minista Alake ya tabbatar da cewa an hanzarta dukkan amincewar da ake buƙata.
Ya ce “zamanin tangal-tangal ya wuce,” tare da umartar hukumomin da abin ya shafa su samar da sahihin tsari cikin sauri wajen bayar da lasisi da takardun mallaka domin aikin ya tafi yadda aka tsara.


