Gabas ta Tsakiya: FAAN Ta Fitar da Gargaɗin Tafiya Sakamakon Tashin Hankuli

Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya, Federal Airports Authority of Nigeria (FAAN), ta sanar da soke da jinkirin wasu jirage zuwa ƙasashen Gabas ta Tsakiya sakamakon rufe sararin samaniya a wasu sassan yankin.

A cikin sanarwar da ta fitar, FAAN ta ce tana sanar da matafiya cewa rufe sararin samaniya a wasu ɓangarorin Gabas ta Tsakiya na ci gaba da shafar zirga-zirgar jirage zuwa da daga yankin.

Rahotanni sun nuna cewa tangardar ta samo asali ne daga tashin hankalin siyasa da na soja tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran, wanda ya ƙara tsananta a ranar Asabar.

Kamfanonin jiragen sama irin su Emirates da Qatar Airways na daga cikin waɗanda lamarin ya shafa, inda wasu daga cikinsu suka dakatar da zirga-zirga zuwa da daga biranen Dubai, Abu Dhabi da Doha.

An shawarci fasinjoji da su tuntubi kamfanonin jiragensu domin samun sabbin bayanai kan halin jiragensu da kuma yiwuwar sake tsara tafiya (rebooking).

FAAN ta ce tana ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki tare da haɗin gwiwar hukumomin sufurin jiragen sama da kamfanonin jirage domin tabbatar da tsaron matafiya.

A gefe guda, gwamnatin Najeriya ta fitar da gargaɗin tsaro ga ‘yan Najeriya da ke zaune a Iran da ƙasashen makwabta a yankin Gulf, sakamakon ƙaruwa a rikicin soja da ke faruwa a yankin.