Biyan Basussukan Da Aka Karɓa Da Danyen Mai Ya Ci N8.36 Tiriliyon a 2025

A shekarar 2025, kusan kashi 14.66 cikin ɗari na jimillar man fetur ɗin da Najeriya ta hako ya tafi wajen biyan basussukan da aka karɓa da jinginar da danyen mai.

Bayanai daga rahotannin kuɗi na NNPC Limited sun nuna cewa manyan yarjejeniyoyin bashi guda huɗu—Project Gazelle, Project Yield, Leopard da Eagle Export Funding—sun ɗaure kusan ganga dubu 213,000 na mai a kowace rana domin biyan bashin.

A cikin shekara guda, wannan ya kai ganga miliyan 77.75. Idan aka ƙiyasta farashin ganga ɗaya a dala $72.08 tare da musayar kuɗi na Naira 1,492 kan dala, darajar kuɗin da aka karkatar domin biyan bashi ta kai kusan Naira tiriliyan 8.36.

Wannan babban adadi ya tafi kai tsaye wajen biyan masu bashi kafin ya shiga asusun gwamnatin ƙasa.
An tsara waɗannan yarjejeniyoyin ne domin magance matsalolin gaggawa, ciki har da gyaran matatun mai da kuma tallafawa kuɗaɗen gudanar da gwamnati.

A wata sanarwa ta NNPC kan yarjejeniyar Eagle Export Funding, an bayyana cewa: “Kuɗin da aka karɓa dole ne a biya su ta hanyar isar da danyen mai… inda aƙalla ganga miliyan 1.8 dole ne a samar a kowane lokacin isarwa.”

Shirin Project Yield, wanda ya taimaka wajen gyaran matatar mai ta Fatakwal, shi ma yana daga cikin manyan basussukan. Wannan bashin na kimanin Naira tiriliyan 1.5 yana buƙatar isar da ganga 67,000 na mai a kowace rana.

Duk da cewa an ba shi ɗan lokaci kafin fara biya, an tsara cewa biyan bashin zai fara ne daga watan Yunin 2025, lamarin da ya ƙara rage adadin man da ƙasar za ta iya sayarwa kai tsaye.
Mafi girman yarjejeniyar ita ce Project Gazelle, wadda aka yi domin samun kuɗi gaba domin biyan haraji da kuɗaɗen sarauta na mai.

A farkon shekarar 2025, bashin da ya rage na wannan shiri ya kai Naira tiriliyan 3.8, kuma yarjejeniyar na buƙatar isar da ganga 90,000 na mai a kowace rana har sai an gama biyan bashin.

Ba danyen mai kaɗai ba, har ma da kuɗaɗen gas suna fuskantar irin wannan matsin. Wata yarjejeniya da Nigeria LNG Limited ta sa an ba Najeriya Naira biliyan 772 a gaba domin samar da gas a nan gaba.

Ya zuwa ƙarshen 2024, har yanzu ana bin daruruwan biliyoyin naira na gas, wanda ya ƙara rikitar da tsarin basussukan da aka jinginar da makamashi.

Masu sukar irin waɗannan yarjejeniyoyi suna nuna rashin bayyananniyar gaskiya a cikinsu. Shugaban kamfanin AHA Strategies, Ademola Adigun, ya ce: “Wasu daga cikin danyen manmu tuni an ɗaure su a yarjejeniyoyin bashi. Matsalar ita ce Najeriya ba ta san cikakkun bayanan waɗannan yarjejeniyoyin ba saboda rashin gaskiya wajen bayyana su.”

Masana tattalin arziƙi sun ce irin waɗannan yarjejeniyoyin da aka yi a baya suna rage damar bunƙasar tattalin arziƙin yanzu.

Daraktan Centre for the Promotion of Private Enterprise (CPPE), Dr. Muda Yusuf, ya bayyana cewa: “A lokacin gwamnatin tsohon gwamnan Babban Banki, Godwin Emefiele, Najeriya ta sayar da danyen mai da yawa tun kafin lokaci. Wadannan yarjejeniyoyin na gaba suna ci gaba da rage kuɗaɗen shiga na yanzu.”

Duk da haka, wasu masana na ganin ana fara samun sauyi a yadda ake tafiyar da harkar. Duk da cewa karkatar da Naira tiriliyan 8.36 na nuna nauyin basussukan da aka karɓa a baya, Yusuf ya ce “a karkashin sabon jagorancin NNPC ana ganin ƙarin ƙwarewa da buɗe-baki,” yana mai cewa bayyana gaskiya gaba ɗaya ne kaɗai zai dawo da amincewar jama’a ga tattalin arziƙin ƙasar.