Rikicin Yankin Gulf: OPEC+ Ta Amince Fitar da Gangar Mai 547,000 a Rana

Ƙungiyar ƙasashen masu fitar da man fetur da abokan hulɗarta, OPEC+, ta amince da ƙara yawan fitar da mai da ganga 547,000 a kowace rana daga watan Satumban 2026, yayin da rikicin yankin Gulf ke barazanar tayar da farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Manyan mambobin ƙungiyar, ƙarƙashin jagorancin Saudiyya da Rasha, za su samar da kusan ganga 206,000 a rana, adadi da ya fi ƙarin gangar 137,000 na wata-wata da aka saba gani a ƙarshen shekarar 2025.

Matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da tashin hankali bayan hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila kan Iran, inda rahotanni suka ce an kashe Jagoran Addini, Ali Khamenei, tare da tangarda zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Strait of Hormuz, wacce ke da muhimmanci wajen jigilar mai.

Wasu daga cikin ƙasashen da ke samar da mai, ciki har da Saudiyya, Iraki, Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), sun riga sun fara ƙara yawan fitar da mai tun watan da ya gabata, kamar yadda suka yi a lokacin hare-haren da aka kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran a watan Yunin bara.

Rikicin yankin Gulf ya rage saurin zirga-zirgar jiragen ruwa, lamarin da ya haifar da damuwa kan ko mambobin ƙungiyar za su iya ci gaba da fitar da karin mai yadda aka tsara duk da ƙarin rabon da aka amince da shi.

A baya, OPEC+ ta dakatar da shirin ƙara yawan mai a farkon kwata na shekarar 2026 domin daidaita kasuwa sakamakon wuce gona da iri a samarwa da kuma rashin tabbas kan man Venezuela.

Masana na cewa sabon matakin ya nuna yadda OPEC+ ke ƙoƙarin daidaita tsakanin tabbatar da wadatar mai a duniya da kuma mayar da martani ga rikice-rikicen siyasa da na tsaro da ka iya tayar da kasuwa.

Kasancewar OPEC+ na da babban kaso a samar da man fetur na duniya, duk wani mataki da ta ɗauka na da tasiri kai tsaye kan sauyin farashi, kuɗaɗen shiga da kuma daidaiton kasuwar mai ta duniya.